Abin da Asibitin Aminu Kano Ya Ce kan Zargin Cire Wa Wata Mata Mahaifa Babu Izininta
- Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya yi martani kan zargin cire wa wata matashiya mahaifa a shekarun baya
- Asibitin ya musanta zargin cire mahaifar ba tare da izini ba, yana mai barranta da rade-radin cewa ba gaskiya ba ne
- Wata mata ta bayyana a gidan rediyon Berekete Family, tana zargin asibitin AKTH da cire mahaifarta ba tare da saninta ba a 2017
- Shugaban asibitin AKTH, Dr. Abdurrahman Abba Sheshe, ya ce an cire mahaifar don ceton rai, bayan samun matsala mai tsanani da ta kai ga mutuwar jariri
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya musanta zargin da ake masa na cewa likitocinsa sun cire mahaifar wata mara lafiya ba tare da izini ba.
Asibitin ya bayyana takaicinsa da kuma zargin a matsayin ƙarya da ake ƙoƙarin yi domin bata sunan cibiyar lafiya.

Source: Facebook
An zargi Asibitin Aminu Kano da cire mahaifa
Shugaban AKTH, Dr. Abdurrahman Abba Sheshe shi ya tabbatar da haka inda ya shawarci al'umma, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Rigimar ta fara ne bayan wata mata ta bayyana a wani shiri na gidan rediyon kare haƙƙin bil’adama mai suna “Berekete Family” ya wallafa a Facebook.
Matashiyar ta yi zargin cewa lokacin da ta haihu a asibitin AKTH a shekarar 2017, an cire mahaifarta ba tare da izinin ta ba.
An yada labarin sosai a kafafen sada zumunta inda al'umma ke kira ga gwamnatin Kano da sauran hukumomi su gudanar da bincike.
Matar ta ce an kwantar da ita a asibitin AKTH don haihuwa a 2017, inda aka ce an yi mata aikin gaggawa bayan faduwar jini.
Ta ce ta farka bayan kwana shida inda aka shaida mata cewa jaririnta ya mutu sannan an cire mahaifarta ba tare da an shaida mata ba.
Asibitin Aminu Kano ya musanta zargin da ake masa
Dr. Sheshe ya ce aikin ya zama dole domin ceton ranta saboda wata matsala mai tsanani da ta kai ga fashewar mahaifa.
Shugaban asibitin ya kuma bayyana cewa jaririn ya riga ya mutu kafin matar ta iso asibitin.
Dr. Sheshe ya ce an samu izinin aikin daga wani, amma ya yarda akwai matsala a tsari saboda sunan wanda ya sanya hannu ba a bayyana ba.
Ya kuma tabbatar da cewa jaririn ya mutu an miƙa shi ga mijin matar don binne shi, kamar yadda ka’idar asibiti ta tanada.
Dr. Sheshe ya yi kira ga jama’a da su daina yaɗa abin da ya kira ƙaryar da aka ƙirƙira domin bata suna.
Asibitin Aminu Kano ya sake aikin ƙwaƙwalwa
A baya, kun ji cewa Asibitin koyarwa na malam Aminu Kano ya yi nasarar gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu inda suka cire wani tsiro.
An gudanar da aikin ne inda aka cire wani tsiro daga kwakwalwar wata baiwar Allah.
An cire tsiro ne daga kwakwalwar wata Malama Nafisa mai shekaru 47 a duniya kuma 'yar asalin jihar Edo.
Asali: Legit.ng

