Asibitin Malam Aminu Kano yayi aikin kwakwalwa karo na biyu cikin nasara

Asibitin Malam Aminu Kano yayi aikin kwakwalwa karo na biyu cikin nasara

Asibitin koyarwa na malam Aminu Kano ya gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu inda suka cire wani tsiro tare da samun nasarar gudanar da wannan aiki. An gudanar da aikin ne inda aka cire wani tsiro daga kwakwalwar wata baiwar Allah.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, aikin kwakwalwar da aka gudanar a asibitin an samu nasara. An cire tsiro ne daga kwakwalwar wata Malama Nafisa mai shekaru 47 a duniya kuma 'yar asalin jihar Edo.

An turo Malama Nafisa ne daga asibitin koyarwa na jihar Legas bayan ta bi wasu matakan jinya a asibitin.

Kwararrun likitoci daga fannoni daban-daban ne suka dukufa akan Malama Nafisa. Aikin ya dauka tsawon sa'o'i biyar ana yinshi amma an samu nasara.

DUBA WANNAN: FG tace babu amincewarta wani tsohon gwamna kuma sanata a yanzu ya shigo da makamai

Babban likitan aikin kwakwalwa na asibitin Malam Aminu Kano, Dr Musbahu Haruna Ahmad ne ya jagoranci aiki. Ya bayyana cewa, sun samu nasarar ne sakamakon taimakon kwararrun likitoci daga fanni daban-daban.

Ya kara da bayyana cewa, sun gudanar da aikin a tsanaki ne inda suka sanya na'ura ta hancin mara lafiyar wanda ya kai har zuwa kwakwalwarta inda ake bukatar yin aikin.

Dr Ahmad ya kara da cewa, sun yi amfani da wasu kamarori masu kama da na hangen nesa tare da wasu fitillun haske wadanda suka taimakawa na'urar da aka saka ta hancinta wajen nuna inda tsiron yake inda suka ciro shi ta hancinta.

Babban likitan ya bayyana cewa, tuni suka sallami Mallama Nafisa bayan da ta shafe kwanaki 6 tana jinya a asibitin kuma suka gamsu da warkewarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel