Ma'aikaciyar jinya ta fallasa likitan da ya cire wa 'yar gudun hijira mahaifa

Ma'aikaciyar jinya ta fallasa likitan da ya cire wa 'yar gudun hijira mahaifa

- Wata ma'aikaciyar jinya tare da wasu lauyoyi sun bankado asirin wani likita a wurin tsare 'yan gudun hijira a Georgia

- Ma'aikaciyar jinyar da kanta ta kai korafin yadda likitan yake cire wa mata 'yan gudun hijira mahaifa ba tare da saninsu ba

- Wani tsohon ma'aikacin wurin tsaron, ya ce Dr Amin ne likitan matan da ke dubasu kuma komai kankantar ciwo aiki yake yi musu

Wata ma'aikaciyar jinya tare da lauyoyi sun tona asirin wani likita da ya cire wa 'yar gudun hijirar mahaifa a inda aka adanata a Georgia da ke Amurka.

Ma'aikaciyar jinyar ta kai korafin zuwa sashi na musamman na tsaron cikin gida da sifeta janar na yankin, Vanguard ta wallafa.

Ma'aikaciyar jinyar mai suna Dawn Wooten, ta zargi cibiyar tsare 'yan gudun hijirar da ke Irwin da bada damar cire wasu sassa masu amfani na jikin jama'ar da suka tsare ba tare da izininsu.

Wooten ta ce, ana tura matan domin samun likitocin da ke cire musu sassa ko kuma dukkan mahaifarsu.

A yayin da Wooten bata bayyana wanne likita bane, lauyoyin matar da aka cire wa mahaifar sun gano cewa Dr Mahendra Amin ne.

An gano cewa Amin ya cigaba da ganin mata daga wurin da aka tsaresu na tsawon shekaru duk da majinyatansa da ke korafi.

An gano likita Amin ne ta hanyar tattaunawa da aka yi da wasu mata biyu da ke tsare.

Yana aiki da asibitin yankin Irwin, inda ake duba marasa lafiya har da wadanda aka tsare.

KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka azabtar da matashi har ya sheka lahira a Nasarawa

Ma'aikatan jinya sun fallasa likitan da ya cire wa 'yar gudun hijira mahaifa
Ma'aikatan jinya sun fallasa likitan da ya cire wa 'yar gudun hijira mahaifa. Hoto daga Vanguard
Source: UGC

KU KARANTA: Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu

Wani ma'aikacin wurin ya tabbatar da cewa Amin ne kadai likitan matan da ke duba matan da aka tsare.

"Abinda na sani shine, idan kaje wurinsa da kowacce irin matsala, sai yace aiki zai yi maka," tsohon ma'aikaci a Irwin yace.

"Ban san abinda yasa haka ba, yana aiki da yawa gaskiya a kan mata," ya kara da cewa.

A martanin Dakta Amin, ya ce sau biyu kacal ya taba yi wa mata babban aiki, kuma a kusan shekaru biyu zuwa uku ne da suka gabata.

A wani labari na daban, Najeriya ta tabbatarwa da 'yan kasar nan da ke gudun hijira a Diffa da ke jamhuriyar Nijar, cewa tana musu shirye-shiryen dawowa gida Najeriya.

Wasu wakilan gwamnatin tarayya da suka zaiyarci kasar, wadanda Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya jagoranta, sun sanar da masu gudun hijirar cewa sun je duba halin da suke ciki domin ganin yadda za a kwashesu tare da dawo da su gida Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel