Yan Najeriya Sun Soki Karin Kudin Kiran Waya da 'Data', Sun Fadi Kason da Ya Dace a Kara

Yan Najeriya Sun Soki Karin Kudin Kiran Waya da 'Data', Sun Fadi Kason da Ya Dace a Kara

  • Kungiyar masu amfani da layukan sadarwa (NATCOMS) ta yi watsi da karin kudin tarho da ta ce bai dace ba kuma zai kara wa mutane wahala
  • Hukumar NCC ta amince da karin kashi 50% bayan rokon kungiyoyin sadarwa saboda wahalhalun aiki da karin kudade a wasu sassa kamar lantarki
  • NATCOMS ta yi barazanar kai maganar kotu, tana mai cewa karin bai dace ba, suna so a rage shi tsakanin 5% zuwa 10%

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar masu amfani da layukan sadarwa (NATCOMS) ta nuna rashin amincewa da karin kudin tarho da 'data' a Najeriya.

Kungiyar ta nuna damuwa tana mai cewa bai dace ba kuma zai kara wa mutane wahalhalu kan wanda suke ciki.

Yan Najeriya sun soki karin kudin kiran waya da na data
Kungiyoyi a Najeriya sun yi fatali da karin kudin kiran waya da data. Hoto: @NgComCommission.
Asali: Twitter

Yawan kudin da yan Najeriya za su kashe

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Channels TV ta ce Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da karin kashi 50% ga kamfanonin sadarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan an lissafa abin da yan Najeriya za su na kashewa da Hukumar NCC ta amince da karin farashin kira zuwa Naira 16.5 a kowace minti.

Bincike ya nuna cewa jimillar kiran gida da aka yi a shekarar 2023 sun kai mintuna biliyan 408.5, inda MTN ta samu kudi kira.

A sabon farashin, ana hasashen MTN za ta samu kudaden shiga da suka haura Naira tiriliyan 4 daga kiran da aka yi da aka karɓa a fadin Najeriya kadai.

Kungiyar NATCOMS ta fusata da karin kudin kira

Matakin ya biyo bayan korafe-korafen kungiyoyin ALTON da ATCON da suka nemi a kara kudin.

Sai dai NATCOMS ta soki wannan matakin, tana mai cewa zai yi wahala ga masu amfani da layukan sadarwa.

Kara karanta wannan

"Ban ƙwallafa rai ba": Peter Obi ya canja shawara kan kudurin zama shugaba ƙasa

Shugaban kungiyar, Deolu Ogunbanjo ya bayyana rashin jin dadinsa game da karin inda ya ce zai dagula lamura.

"Wannan ba abu ne da bai dace ba, talakawa na fama da wahala sosai, kuma karin zai tsananta musu."
"Wannan abu ne da ba za mu amince da shi ba kwata-kwata musamman a wannan hali da ake ciki."

- Cewar kungiyar

NATCOMS za ta dauki matakin shari'a

Kungiyoyin sadarwa sun nemi karin kashi 100% saboda tsadar aiki da karin kudade a wasu fannoni, suna cewa hakan zai inganta ayyukansu.

Shugaban MTN Nigeria, Karl Toriola, ya ce karin zai taimaka wajen bunkasa ayyukan sadarwa, da inganta ayyukansu ga 'yan Najeriya.

Sai dai NATCOMS ba ta gamsu ba, tana mai cewa akwai wasu hanyoyin da za a bi, kamar kara tsakanin kashi 5% zuwa 10% kawai, cewar rahoton The Guardian.

Shugaban NATCOMS ya ce ba a cimma yarjejeniya kan karin ba, yana mai barazanar daukar matakin shari’a kan lamarin.

Kara karanta wannan

Karin kudin kira: Farfesa Pantami ya fadi yadda barinsa ofis ya yi wa wasu dadi

Tattaunawar Legit Hausa da dan kasuwa

Muhammad Salisu Shuaibu da ke harkar siyar da katin waya da tura data ya koka kan lamarin.

Shuaibu ya ce ko a yanzu da suka kara kudin 1GB zuwa N350 mutane sun fara neman sauki ta wasu hanyoyi.

"A gaskiya karin nan zai iya shafar kasuwancinmu saboda a da 1GB N300 amma yanzu N350 kuma mun fahimci mutane sun fara ja baya."

- Salisu Shuaibu

Dan kasuwar ya ce to ya za su yi idan har aka kara zuwa N400 ko N500 da wasu ke hasashe.

Hukumar NCC ta kara kudin kira

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta hannun hukumar sadarwa ta ƙasa watau NCC ta amince kamfanonin sadarwa su ƙara kudin kira da kaso 50%.

Mai magana da yawun NCC, Reuben Mouka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 20 ga watan Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Karin kudin kira: NLC za ta saka kafar wando daya da gwamnatin Tinubu

Tun farko kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel da Glo sun bukaci a ba su dama su nunka kuɗim kiran waya, lamarin da NCC ta ce ya yi yawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.