Ragargazar Sojoji Ta Birkita Turji, Dan Ta'addan Ya ba da Mamaki bayan Sakin Mutane
- Lamura sai kara dagulewa Bello Turji suke yi tun bayan hare-haren da rundunar sojoji ke kai masa a yan kwanakin nan a yankin Arewacin Najeriya
- An tabbatar cewa shugaban ƴan bindiga, Bello Turji ya saki dukkan waɗanda ya kama yayin da sojoji ke matsa masa lamba a jihar Zamfara
- Majiyoyin sirri sun ce Turji ya saki mutanen ne saboda hare-haren sama da ƙasa da sojojin Najeriya ke kaiwa a mafakarsa da kuma mayakansa
- Ana ganin wannan matakin na Turji na daga cikin dabarun kaucewa ƙarin rikici ne yayin da sojoji suka lashi takobin cafkarsa da rai ko matacce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Gusau, Zamfara - A cikin wani lamari mai ban mamaki, shugaban ƴan bindiga mai suna Bello Turji ya saki duk mutanen da ƙungiyarsa ta kama.
Hakan na zuwa ne yayin da sojojin Najeriya suka ƙara kaimi wajen farautarsa da kakkabe ƴan bindigar da ke tare da shi a Jihar Zamfara.

Asali: Original
Turji ya yi hijira zuwa karamar hukumar Maradun
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa dan ta'addan na fuskantar barazana daga sojoji a cikin yan kwanakin nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni suka tabbatar ana zargin cewa shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, yana cikin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara yayin da sojoji suka kara matsa masa.
Rahotanni sun ce an ga mabiyan Turji suna hijira a kan babura, dauke da raunana, zuwa wuraren Garsa/Kadanya a ranar 19 da 20 ga watan Janairun 2025.
An yi zargin cewa Turji yana boye tare da wasu mabiyansa a Garsa/Kadanya, tare da goyon bayan tsohon abokin gaba, Jummo Smally.
Hakan bai rasa nasaba da matsin lamba daga rundunar sojoji da Bello Turji ke fuskanta da mayakansa.
Bello Turji ya razana da hare-haren sojoji
Majiyoyin sirri sun shaida cewa dalilin sakin mutanen na da alaƙa da matsin lamba daga sojojin Najeriya a ƙarƙashin Operation Hadarin Daji da Operation Forest Sanity.
Hare-haren sama da ƙasa da ake kaiwa mafakarsa a Fakai, Shinkafi da sauran yankuna sun raunana ƙungiyarsa, lamarin da ya sa suka koma baya.
Ana kallon sakin waɗanda aka kama a matsayin dabarar kaucewa ƙarin rikici ko yin arangama da jami'an tsaro da ke ƙara matsowa kusa da shi, cewar Daily Post.
Tun farko, rundunar sojojin Nigeriya ta lashi takobin cafke shi ko dai a raye ko a mace yayin da ta ce tana samun nasara a yaki da yan bindiga.
Bello Turji ya shirya kalubalantar sojoji a Zamfara
A baya, kun ji cewa awanni da kashe dansa, Bello Turji ya kafa sabon sansani a dajin Dutsi da Yan Buki bayan tafka mummunar asara a hare-haren sojoji.

Kara karanta wannan
Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin
Rahoto ya bayyana cewa Bello Turji ya mayar da sabon sansanin matsayin matattarar 'yan ta'adda da kula da wadanda aka raunata.
Rundunar sojoji na ci gaba da samun nasarorin murkushe 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma a karkashin Operation Fansan Yanma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng