Yan Sanda Sun Kashe Gaggan 'Yan Bindiga 7 a Katsina, Sun Ceto Yara 207

Yan Sanda Sun Kashe Gaggan 'Yan Bindiga 7 a Katsina, Sun Ceto Yara 207

  • 'Yan sanda sun dakile hare-haren 'yan bindiga a jihohi biyu tare da cafke wasu da ke da alaka da ta’addanci da fashi da makami
  • Rundunar 'yan sanda ta ceto yara 207 daga hannun masu safarar yara a Najeriya, ciki har da yara 14 a jihar Ondo da ke Kudancin kasar nan
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an 'yan sanda sun gano makamai, alburusai, da dabbobin da aka sace a jihohin Kogi da Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da nasarori a yunkurinta na yaki da aikata laifuffuka a fadin kasa, ta hanyar amfani da dabarun bincike na zamani.

A cikin wata sanarwa, kakakin yan sanda na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun dakile hare-haren ‘yan bindiga a jihohin Kogi da Katsina.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Yan sanda
'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 7 a Katsina. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A sakon da rundunar 'yan sanda ta wallafa a Facebook, ta sanar da cewa ta cafke wadanda ake zargi da aikata laifukan fashi, garkuwa da mutane da safarar yara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun dakile hare-hare a Kogi

A ranar 18 ga watan Janairu, jami’an ‘yan sanda a Jihar Kogi sun samu labarin wani taron sirri da ‘yan bindiga suka yi a cikin daji da ke Budon, domin tsara harin ta’addanci.

Nan take, jami’an suka tashi zuwa wurin, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar da ake zaton masu garkuwa da mutane ne.

Bayan musayar wuta, an kashe daya daga cikin ‘yan ta'addar, an kama hudu, kuma an gano AK-47 daya, harsashi 30, da babura biyu.

An yabawa jami'an tsaro bisa nasarar, inda aka ce ta nuna irin jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

An kashe 'yan bindiga 7 a jihar Katsina

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

A ranar da aka samu nasarar a Kogi, jami’an ‘yan sanda a Katsina sun yi nasara wajen dakile harin da wasu ‘yan bindiga suka shirya kai wa Ruwan Doruwa, karamar hukumar Dutsinma.

Bayan samun kiran gaggawa, jami’ai sun yi hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, suka yi artabu da ‘yan bindigar har suka kashe bakwai daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere.

An kuma gano dabbobi 109 da aka sace, wanda hakan ya kawo farin ciki ga jama’ar yankin da suka yi addu’a ga jami’an tsaro.

Ceton yara 207 daga hannun masu safara

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ceto yara 207 daga hannun masu safarar mutane a fadin kasa.

A Jihar Ondo, jami’an ‘yan sanda sun cafke wani gungu na masu satar yara a Okuta Elerin-Nla, Akure.

An cafke Abosede Olanipekun, Lukman Isiaka, da Sabira Izuorah, tare da ceto yara 14 masu shekaru tsakanin mako daya zuwa shekara bakwai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Ana ganin nasarar ta nuna yadda rundunar ke ci gaba da yaki da masu aikata laifuffukan da suka shafi safarar yara da yin amfani da su wajen miyagun ayyuka.

Kiran rundunar ‘yan sanda ga jama’a

Rundunar ‘yan sanda ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da cewa masu aikata laifuka sun fuskanci hukunci.

Rundunar ta yi kira ga ‘yan kasa su rika bayar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro domin inganta tsaro a kasar.

Sojoji sun ce Bello Turji ya ji tsoro

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun bayyana cewa Bello Turji ya tsare ya bar dansa yayin da suka kai masa farmaki.

Kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya ce dan ta'addar matsoraci ne tun da ya gudu, ya bar mayakansa aka kashe su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng