An Shiga Tashin Hankali a Katsina: Ƴan Bindiga Sun Harbi Likita, Sun Sace Mutane

An Shiga Tashin Hankali a Katsina: Ƴan Bindiga Sun Harbi Likita, Sun Sace Mutane

  • Ƴan bindiga sun kai wani hari a babban asibitin Kankara da ke jihar Katsina inda suka suka likita tare da sace mutane biyar
  • An rahoto cewa likitan da aka harba, Dakta Murtala Sale Dandashire ya kasance dalibi mafi hazaka a jami'ar ABU a shekarar 2019
  • An ce jami'an tsaro sun bi bayan 'yan bindigar domin kwato wadanda aka sace, yayin da jama'ar Kankara ke cikin firgicin harin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Ƴan bindiga sun kai hari a babban asibitin Kankara da ke jihar Katsina, a daren ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2025.

Wannan harin na zuwa ne kwanakin kadan bayan da 'yan bindigar suka kai makamancin harin a manyan asibitocin Kurfi da Dustinma.

Mazauna Katsina sun shiga firgici yayin da 'yan bindiga suka kai hari babban asibitin Kankara
'Yan bindiga sun harbi likita, sun sace mutum 5 da suka kai hari asibitin Katsina. Hoto: @DanKatsina50
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun kai hari a asibitin Katsina

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa maharan sun shiga asibitin dauke da makamai, suka yi garkuwa da mutane da dama a cewar rahoton Bakatsine a X.

Kara karanta wannan

Sojoji sun illata Bello Turji bayan hallaka ɗansa, an jiyo shi yana neman agajin yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bakatsine, wanda mai sharhi kan lamuran tsaro a shiyyar Arewa maso Yamma, ya sanar da cewa 'yan bindigar sun harbi wani likita yayin farmakin.

An harbi Dr. Murtala Sale Dandashire

Rahoton ya nuna cewa an harbi likitan mai suna Dakta Murtala Sale Dandashire a cinya kuma a yanzu yana karbar kulawa daga takwarorinsa a asibitin.

Dakta Murtala Saleh Dandashire, dan asalin Kankara, shi ne dalibin da ya fi kowa hazaka a makarantar koyon likitanci ta jami'ar ABU da ke Zariya a shekarar 2019.

Likitan ya samu lambobin yabo saboda kwarewar da ya nuna a jarrabawowi a kan ilmin fida, kimiyyar jini da ilmin aikin halittu da makamantansu.

Jami'an tsaro sun bi sahun 'yan bindigar

An ce 'yan bindigar sun kuma yi awon gaba da kimanin mutane biyar bayan da suka harbi likitan, lamarin da ya jefa jama'a a cikin firgici.

Hakazalika, wani mai bayar da rahoto daga jihar Katsina, Muhammad Aminu Kabir ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa 'yan bindigar sun yi harbe-harbe a asibitin.

Kara karanta wannan

"Ba za mu yafe ba": Iyalan wadanda sojoji suka kashe a Zamfara sun fara neman diyya

Muhammad Kabir ya rahoto wani mazaunin yankin na cewa:

“Mun ji ƙarar harbe-harbe da hayaniya daga asibitin, wanda ya jefa mutane cikin tsananin firgici.”

Kabir ya ce va a tabbatar da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba tukunna, amma jami’an tsaro sun fara bin sawun maharan domin ceto wadanda aka sace..

Mazauna Katsina sun shiga cikin firgici

Hukumomi sun tabbatar da tura jami’an tsaro don tabbatar da tsaro a yankin da kuma kare rayukan jama’a daga karin hare-hare.

Wannan hari a cewar mazaunin jihar ta Katsina ya kara dagula lamuran tsaro a yankin Kankara, wanda ya daɗe yana fama da hare-haren ƴan bindiga.

Al’umma sun bayyana damuwa kan matsalar tsaro da ta zama babbar barazana ga rayuka da dukiyoyinsu a jihar Katsina.

Tsokaci daga Nura Haruna Maikarfe

Nura Haruna Maikarfe, mai fashin baki kan tsaro a jihar Katsina, ya nuna damuwarsa kan harin da ’yan bindiga suka kai Babban Asibitin Kankara.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba da 'yan sanda suka mamaye sakatariyar PDP, sun rufe hanyar shiga ofis

“Harin da aka kai asibitin Kankara hari ne kai tsaye kan fannin lafiya, wanda ya zama wajibi gwamnati da jami'an tsaro su dauki matakin gaggawa," inji Maikarfe.

Yayin da yake kara bayani, ya nuna yadda rashin tsaro ke kawo illa ga manyan bangarori kamar kiwon lafiya, ilimi, da jin dadin al’umma a Katsina.

Nura Haruna ya ce:

“Idan ’yan bindiga suka fara kai hari ga asibitoci da makarantu, wannan yana nuna cewa babu wurin da ke da tsaro ga jama'a, musamman dalibai da marasa lafiya."

Maikarfe ya yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen magance matsalar tsaro tare da tabbatar da zaman lafiya ga al’ummar Katsina.

“Tsaro hakki ne na kowa. Dole ne gwamnati, hukumomin tsaro da ’yan kasa su yi aiki tare don kare jiharmu daga barazanar 'yan ta'adda,” in ji Maikarfe.

'Yan bindiga sun kai hari asibitin Kurfi

Tun da fari, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai hari babban asibitin Kurfi, Katsina cikin dare kwanakin baya, suka harbi mai gadi tare da sace mata hudu.

Kara karanta wannan

Yaki da rashin aikin yi: Gwamna zai dauki ma'aikata 3,000

An ce cikin waɗanda aka sace har da matar likitan asibitin mai aikin dare kuma ana ganin wannan hari a matsayin koma baya ga ƙoƙarin tsaron mutanen garin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.