'Akwai Alheri': Gwamna Ya Fadi Albarkar da Ke cikin Cire Tallafin Mai, Ya Shawarci Gwamnoni
- Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya yi magana kan alherin da gwamnoni suke samu bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023
- Uzodinma ya ce cire tallafin man fetur rahama ne ga gwamnatocin jihohi don samun karin kudi saboda gudanar ayyukan ci gaba a jihohinsu
- Gwamnan ya bayyana cewa cire tallafin ya kawo karin kudi ga jihohi, wanda zai taimaka wajen bunkasa ababen more rayuwa da jin dadi
- Ya bukaci jihohi su yi amfani da karin kudaden don tabbatar da cigaban jama’a, musamman bayan cire tallafin da Gwamnatin Tarayya ta yi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Owerri, Imo - Duk da korafe-korafe daga al'ummar Najeriya, Gwamna Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya fadi alherin da cire tallafin man fetur ya jawo musu.
Gwamna Uzodinma ya bayyana cewa cire tallafin man fetur wata babbar rahama ce ga gwamnatocin jihohin Najeriya saboda alherin da suke samu.
Channels TV ta ce Gwamnan ya yi wannan bayani ne a jiya Litinin 13 ga watan Janairun 2024 a Imo yayin duba wasu ayyuka domin bikin cika shekara guda a wa’adin sa na biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya magantu bayan cire tallafin mai
Hakan ya biyo bayan maganar da shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake yi game da cire tallafin mai a yayin jawabinsa ga yan kasa.
A yayin jawabin, Tinubu ya ce babu nadama kan cire tallafin man fetur a watan Mayu 2023 da ya yi a Najeriya.
Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin ya kawo gasa a bangaren man fetur, inda farashin ya fara raguwa a wurare daban-daban.
Ya jaddada cewa bai aminta da kayyade farashi ba, yana mai cewa za a ci gaba da kokarin samar da isasshen fetur.
Gwamna ya fadi alherin cire tallafin mai
A cewarsa, wannan matakin ya ba da damar samun karin kudi ga jihohi don yin aiki mai ma’ana wajen cigaban al’umma da jihohinsu.
Uzodinma ya bayyana cewa karin kudaden da ake samu yanzu zai taimaka wajen samar da kayayyakin more rayuwa, habaka kasuwanci, da jin dadin jama’a.
Gwamnan na APC ya kara da cewa jihohi yanzu suna da damar yin aiki da karin kudin da suka samu daga cire tallafin man fetur, cewar Daily Post.
Ya yi kira ga gwamnatocin jihohi su tabbatar sun yi ayyukan da za su amfani al’umma, duba da karin kudaden da suke samu daga gwamnati.
Gwamnan ya ba yan kasa shawara kan haraji
A baya, kun ji cewa Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya yi kira ga ƴan Najeriya su ware lokaci su karanta baki ɗaya abin da ke kunshe a kudirin harajin Bola Tinubu.
Hope Uzodinma ya ce bai dace mutane su tsaya suna sukar kudirin a cikin duhu ba tare da sanin alherin ko akasin haka da ya ƙunsa ba.
Gwamnan ya bayyana cewa a ganinsa kudirin yana da amfani domin wani tsari ne da zai kawo ƙarin kuɗin shiga ga gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng