Kotu Ta Saki Mubarak Bala, Matashin da Aka Daure kan Zargin Batanci ga Addini
- Kotu ta saki Mubarak Bala bayan shafe shekaru hudu a gidan yari sakamakon kama shi da laifin batanci ga Annabi SAW da sukar addini
- Wata kotun daukaka kara ta rage hukuncin Mubarak Bala bayan an bayyana cewa hukuncin farko na shekaru 24 ya yi tsauri
- A wani bidiyo da ya nuna lokacin da Mubarak Bala ke fitowa daga gidan yarin, matashin ya ce yana fargabar za a iya sake farmakarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mubarak Bala, matashin Najeriyar nan da ya shahara a sukar addini, ya bayyana fargaba bayan sakinsa daga kurkuku.
Mubarak dai ya shafe tsawon shekaru hudu a gidan yari tun bayan da aka yanke masa hukunci kan tuhume-tuhumen batanci ga Annabi.
Yadda aka daure Mubarak Bala a gidan yari
A wani bidiyo da jaridar BBC ta wallafa a ranar Talata, 7 ga watan Janairun 2024, Mubarak ya ce yanzu bai san ya lamarin tsaronsa zai kasance ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama Mubarak, shugaban kungiyar HAN, a ranar 28 ga Afrilu 2020 a gidansa na Kaduna, inda aka kai shi Kano bayan korafe-korafen da suka yi yawa a kansa.
An dai zargi Mubarak Bala da tayar da hankulan al'ummar Musulmi a wancan lokaci.
A 2022, babbar kotun Kano ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 24 a kurkuku bayan ya amsa laifukan batanci ga addini da tayar da fitina.
Duk da haka, kotun daukaka kara ta rage masa hukuncin, ta ce hukuncin ya yi tsauri da yawa.
Kotu ta saki Mubarak Bala daga kurkuku
Da yake magana da manema labarai bayan sakinsa, Mubarak Bala ya ce, “Ina da ’yanci yanzu, amma akwai barazana da zan fuskanta daga yanzu.”
Ya kara da cewa yana cike da damuwa kan tsaron rayuwarsa a yanzu, tun da akwai wadanda suka kullace shi a zamansa a gidan yarin.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya amsa laifin, Mubarak Bala ya bayyana cewa ya yi hakan ne domin kare kansa da masu wakiltarsa.
Matashin ya ce:
“Na yi imanin amsa laifina a lokacin ya ceci ba iya rayuwata ba, har ma da mutanen jihar, musamman wadanda ke da alaka da shari’ata.”
Dalilin daukaka karar hukuncin Mubarak
An daukaka kara kan hukuncin Mubarak Bala kan dalilai hudu: Rashin hurumin babbar kotun Kano da rashin adalci a hukuncin alkalin.
Sauran dalilan sun hada da gazawar kotu na bai wa Bala fa'idar neman sassauci kan amsa laifin da ya yi kuma kin amfani da doka yadda ya dace wajen yanke masa hukunci.
Shari’ar ta jawo hankalin duniya, inda kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka nuna damuwa game da tsaronsa da kuma ‘yancin fadin albarkacin baki a Najeriya.
Abin da mutane suka ce kan daure Mubarak
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan hukuncin daurin shekaru 24 da aka yanke wa Mubarak Bala kan batanci.
Wasu sun kalubalanci amfani da dokokin addini wurin hukunta wanda ya bar addini, yayin da wasu ke ganin hukuncin kisa ya fi dacewa da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng