Wani Shahararren Ɗan Sandan Najeriya Ya Musulunta, Ya Canja Suna zuwa Muhammad
- Rahotanni sun nuna cewa ACP Daniel Itse Amah ya karbi addinin Musulunci, inda ya sauya sunansa daga zuwa Muhammad a jiya
- A lokacin da yake matsayin DPO a Kano, an ce ACP Muhammad ya kyautatawa daurarru, har ma ya gina masallaci a ofishin Bompai
- ACP Muhammad ya samu lambar yabo da karin matsayi a 2022 bayan kin karbar rashawar dala 200,000 daga masu aikata laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A makon nan ne kafofin sada zumunta suka cika da labaran ACP Daniel Itse Amah, wani shahararren dan sandan Najeriya da ya Musulunta.
An rahoto cewa ACP Daniel, wanda mataimakin kwamishina 'yan sandan ne a Kano ya Musulunta kuma ya sauya suna zuwa Muhammad.
Kano: Dan sandan Najeriya ya Musulunta
Fitaccen dan jaridar nan na Kano, Nasiru Salisu Zango ne ya sanar da wannan labarin a shafinsa na Facebook a ranar 6 ga Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasiru Salisu Zango, ya wallafa cewa:
"Amininmu, dan uwanmu, mataimakin kwamishinan ’yan sanda, ACP Daniel Amah ya karbi addinin Musulunci.
"Dama ACP Daniel mutumin kirki ne a dabi’a wanda duk wanda ya yi mu’amala da shi zai bayyana kyawawan dabi’unsa.
"Zamanin yana DPO a caji ofis din Bompai har katifa yake sakawa wadanda suke kulle a caji ofis dinsa, bayan tsafta da rashin muzgunawa daurarru."
Dan jaridar ya ce ko da can ACP Daniel wanda yanzu ya koma ACP Muhammad ya taba gina masallaci a caji ofis din na Bompai.
Wasu daga cikin ayyukan 'dan sandan
An haifi ACP Daniel Itse Amah (yanzu Muhammad), a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1981, a garin Fobur, da ke karamar hukumar Jos ta Gabas, jihar Filato.
Rahoton jaridar Tribune ya nuna cewa ACP Muhammad ya shiga aikin dan sandan Najeriya a matsayin Cadet Inspector a ranar 15 ga Agusta, 2002.
A matsayin DPO na ofishin 'yan sandan Nasarawa, a jihar Kano, ACP Muhammad ya nuna kwarewa da gaskiya wajen gudanar da ayyukansa.
ACP Amah (Muhammad) ya samu lambar yabo
A ranar 14 ga Afrilu, 2022, ACP Amah ya samu tayin rashawa na dala 200,000 daga masu aikata laifi, amma ya ƙi karɓar tayin, inji rahoton Daily Trust.
A watan Oktoba, 2022, aka karrama shi da lambar yabo ta Public Service Integrity a wani taro da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Sakamakon kin karbar rashawa, an karawa jami'in matsayi daga CSP zuwa mataimakin kwamishinan 'yan sanda (ACP) a watan Nuwamba, 2022.
Bature ya Musulunta bayan zuwa Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Dakta Andrea Brigaglia, wani bature daga Italiya, ya Musulunta sakamakon sha'awar Hausa da Hausawa.
A kokarinsa na yin bincike, Dakta Brigaglia, wanda ya kware a harshen Hausa, ya zauna da Hausawa sosai, wannan ya taimaka masa wajen fahimtar su.
A shekarar 2022, Brigaglia ya karbi addinin Musulunci, yana mai cewa bai da uzuri na ci gaba da zama Kirista bayan fahimtarsa da rayuwar Sufanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng