Shugaba Buhari Ya Baiwa Dan Sandan Da Yaki Karban Cin Hancin $200,000 Lambar Yabo

Shugaba Buhari Ya Baiwa Dan Sandan Da Yaki Karban Cin Hancin $200,000 Lambar Yabo

  • Duk da irin kallo da wasu al'umma ke yi wa jami'an ƴan sanda wajen karɓar cin-hanci da rashawa.
  • Wani Sufurtandan ƴan sanda ya yi watsi da tayin cin-hanci na maƙudan kuɗaɗen dalolon Amurka
  • Kuma a sakamakon haka ne, shugaba Buhari ya yi masa wata babbar kyauta kuma yace ayi koyi da shi

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama wani Sufurtandan ƴan sanda Daniel Amah da lambar yabo saboda namijin ƙoƙari da ya yi wajen yin aiki da gaskiya a yayin gudanar da aikinsa.

A karrama Amah ɗan asalin jihar Fulato ne a wajen wani taro karo na huɗu a Abuja game da taro kan Rage ciin-hanci da rashawa mai taken "Cin-Hanci a Fannin Ilimin".

Kara karanta wannan

An Tabbatar Da Mutawar Mutum 4 Yan Gida Daya Bayan Cin Amala a Jihar Kogi

Amah dai shi ne Shugaban Reshen Hukumar Ƴan Sanda (DPO) da ke Bompai a jihar Kano bayan ƙin karɓar zunzurutun kuɗi har na Dalar Amurka dubu ɗari biyu da aka ba shi a matsayin cin-hanci da rashawa domin ɓatar da wani magunmagun da wani malam Ali Zaki wanda da ke aiki a Bureau De Change Operator bayan haɗa kai da wasu mutane domin yi wa wasu mutane sata na jimilar kuɗi da suka kai Dalar Amurka dubu bakwai da hamsin.

Good guy
Shugaba Buhari Ya Baiwa Dan Sandan Da Yaki Karban Cin Hancin $200,000 Lambar Yabo
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amah shi ne wanda ya kula da wannan tuhuma tare da yin watsi da tayin cin-hanci na dala dubu biyu domin a rufe ƙyas ɗin.

A yayin jawabinsa, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yaba wa wanda aka karrama saboda wannan nagarta tare da amfani da wannan dama domin kira ga sauran ƴan Najeriya da su yi koyi da kyakkyawan aiki, tare da cewa; "akwai buƙatar mu kawar da cin-hanci domin ciyar da ƙasar nan gaba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel