IGP Ya Karrama DPO A Jihar Kano Saboda Yaki Karbar Cin Hancin Makudan Daloli Da Aka Bashi

IGP Ya Karrama DPO A Jihar Kano Saboda Yaki Karbar Cin Hancin Makudan Daloli Da Aka Bashi

  • Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Alkali Baba ya karrama wani DPO a jihar Kano da lambar yabo saboda yaki karban cin hanci
  • Jami'an Yansanda sun kama wani babban lauya mazaunin jihar Kano da wasu yansanda da laifin fashi da makami
  • IGP alkali Baba ya da umarnin a cigaba da gudanar binciken yan fashin da aka kama a hedikwatar yansanda dake Abuja

Abuja - Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya karrama DPO na Unguwar Nasarawa dake jihar Kano SP Daniel Itse Amah, da Satifiket din lambar yabo. Rahoton THE NATION

DPO na Unguwar Nasarawa SP Daniel, ya nuna bajinta da kwarewa a aikin sa, yayin da ya ki karba cin hancin dala USD 200,000 da aka bashi akan kamun wasu yan fashi da makami.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Matashin da ya durawa kabarin mahaifiyar abokinsa ashariya ya shiga hannu

A wata wasika dake kunshe da karramawa, IGP ya jinjinawa SP Daneil da ya nuna kwarewa da bajinta wajen kama wani babban lauya mazaunin jihar Kano, Ali Zaki da wasu yansanda.

Police
IGP Ya Karrama DPO A Jihar Kano Saboda Yaki Karbar Cin Hanci Platinum Post.NG
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna binciken da jami’an yansanda dake karkashin SP Daniel suka gudanar ya kai ga kama kungiyar wasu yan fashi da makami a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka an mayar da shariar hedikwatar yansanda Najeriya dake Abuja bisa umarnin Sufeto Janar na yansanda dan cigaba da gudanar da bincike a boye kamar yadda Tribune Oline ta rawaito

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da kamun da aka yi.

Buratai ya Maka Sowore Kotu, Yayin Da Ya Nemi Diyyar Biliyan N10bn Dan Bata Sunan Shi

A wani labari kuma, tsohon hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya maka mawallafin jaridar Saharar Reporters Omoyele Sowore a gaban wata babbar kotun tarayya dake birnin tarayya bisa zargin buga labaran karya akan shi. Rahoton LEADERSHIP

Buratai na neman diyyar Naira biliyan 10 ne saboda a cewarsa, Sowore, mawallafin jaridar Sahara Reporters, ta yanar gizo da ke Amurka, ya alakanta shi da wani rahoto da ke cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC, ta gano biliyoyin kudade na gida da na kasashen waje a wani gida sa dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel