An Shiga Tashin Hankali a Kwara: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Malamin Jami'a
- Masu garkuwa sun sace Farfesa John Ebeh na jami’ar Prince Abubakar Audu, Anyigba, a kofar gidansa da ke Agbeji, Jihar Kogi
- ‘Yan bindigar sun nemi Naira miliyan 10 daga iyalansa, bayan sun yi awon gaba da shi yayin da suka farmaki anguwar Agbeji
- Rundunar ‘yan sanda ta Kogi ba ta bayar da bayani kan lamarin ba, yayin da abokan aikinsa suka shiga damuwa kan lamarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sace Farfesa John Ebeh na sashen falsafa, jami’ar Prince Abubakar Audu da ke Anyigba (PAAU).
Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Farfesan da ke Agbeji, kusa da Anyigba a karamar hukumar Dekina da misalin karfe 7 na dare.
'Yan bindiga sun sace Farfesa a Kogi
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa sun yi harbe-harbe kan mai uwa da wabi don tsoratar da jama’a kafin su yi awon gaba da malamin zuwa cikin jeji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani makwabcin Farfesan mai suna Akpai ya ce:
“Mun ga wata mota tana bin motarsa da sauri. Mun dauka abokinsa ne sai muka ji harbe-harbe.”
Wani dan uwan Farfesan ya ce an sace shi ne a bakin kofar gidansa da ke kan hanyar Anyigba-Ochadamu-Itobe lokacin da yake dawowa daga cikin gari.
'Yan bindiga na neman N10m kudin fansa
Ya bayyana cewa Farfesan ya riga ya aika wa gidansa da sakon a bude masa kofa kafin ‘yan bindigar suka yi masa kofar rago.
"Yan bindigar sun fara harbe-harbe, suka tsayar da motarsa tare da amfani da wata mota don toshe hanya. Daga nan suka tafi da shi ta karfin tsiya."
- A cewarsa dan uwan malamin.
A cewar dangin malamin, masu garkuwan sun kira waya a ranar Juma’a da daddare, suna neman kudin fansa har Naira miliyan 10.
Abokan aikin malamin sun damu sosai
Har zuwa yanzu, mahukuntan jami’ar ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba, amma wani abokin aikin Farfesan ya bayyana damuwa sosai kan abin da ya faru.
Abokin aikin ya ce:
“Satar Farfesan ta girgiza mu sosai. Na ziyarci iyalansa don jajantawa game da abin da ya faru da shi.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, bai amsa kira ko sakonni ba kan garkuwar da aka yi da Farfesan har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
'Yan bindiga sun halaka wani Farfesa
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe Farfesa Illisan Olowojobi Yinka, malamin Jami’ar Babcock, a wurin taro da ke Iperu, jihar Ogun.
Harin ya faru a mahaifar Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, inda ‘yan bindigar suka sace wasu mutane biyu, suna firgitar da mahalarta taron.
Kakakin ‘yan sanda, SP Omolola Odutola, ta ce an kama wani jami’in tsaro da ya fara aiki makonni biyu kafin faruwar lamarin.
Asali: Legit.ng