Da Dumi-Dumi: Ƴan Bindiga Sun Sace Farfesa Da Mijinta a Gidansu
- Wasu yan bindiga sun kutsa gidan wata Farfesa a Filato sun sace ta da mijinta
- Wani Makwabcin Farfesan mai suna Philips Dachung ya bada labarin yadda lamarin ya faru
- Jami'ar Jos da ke jihar Filato inda Farfesan ke aiki ita ma ta tabbatar da sace matar da mijinta
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wata Farfesa a tsangayar nazarin kananan halittu a Jami'ar Jos mai suna Grace Ayanbimpe, The Punch ta ruwaito.
An gano cewa yan bindigan sun afka gidanta sun sace farfesan ne a safiyar ranar Litinin tare da mijinta a gidansu da ke bayan Haske Quaters, Lamingo, a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar.
DUBA WANNAN: Falaɗinawa Sun Harbo Mana Roka 3,150 Daga Gaza, Isra'ila
Wani mazaunin unguwar mai suna Philips Dachung ya tabbatarwa wakilin majiyar Legit.ng afkuwar lamarin a Jos a ranar Litinin.
Dachung ya ce, "Masu garkuwar sun shiga gidan misalin karfe 2 na dare. Sun kutsa cikin gidan suna harbe-harbe a iska. Makwabta sun razana saboda harbe-harbe hakan yasa ba su kai mata dauki ba.
"Don haka,da safen nan, mun gano an sace farfesan da mijinta. Ba mu san inda suke ba."
Wani ma'aikacin Jami'ar Jos, wanda shima ya tabbatar da lamarin ya ce, "A safen nan mun samu labarin cewa an sace Farfesa Grace Ayanbimpe na Tsangayar Nazarin Kananan Halittu tare da mijinta a gidansu.
"Don Allah ku taya mu addu'a a sako su lafiya, Allah yasa muga karshen matsalar rashin tsaro a kasar nan."
A wani labarin daban, jami'an yan sanda sun halaka a kalla yan ta'addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata, PRNigeria ta ruwaito.
Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan. 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri.
Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta'addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.
Asali: Legit.ng