Masu garkuwa sun sace farfesa yayinda ya tafi kai yaransa makaranta a Nasarawa

Masu garkuwa sun sace farfesa yayinda ya tafi kai yaransa makaranta a Nasarawa

- Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban jami'ar Anchor University, Farfesa Johnson Fatokun

- Masu garkuwar sun tare farfesan ne a hanyar Jos zuwa Nasarawa inda zai tafi filayen tashin jirage ya koma Legas

- Farfesan da ke aiki a Legas ya tafi kai yaransa biyu da ke karatu a arewa ne inda lamarin ya ritsa da shi

Masu garkuwa da mutane sun sace mataimakin shugaban Jami'ar Anchor University, mallakar cocin Deeper Life da ke Jihar Legas, Farfesa Johnson Fatokun, The Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda abin ya faru da shi ya bar Legas a ranar Lahadi domin zuwa arewa don kai yaransa biyu makaranta.

Masu garkuwa sun sace mataimakin shugaban jami'a a Nasarawa
Masu garkuwa sun sace mataimakin shugaban jami'a a Nasarawa. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

An ce yana hanyarsa ta dawowa Legas a ranar Litinin ne yan bindiga suka tare motarsa a hanyar Nasarawa zuwa filin tashin jiragen sama domin dawowa Legas.

Wani majiya ya ce wadanda suka sace shi suna sanye da kaya ne irin ta yan sanda.

Majiyar ta ce, "Farfesan ya kai yaronsa Deeper Life High School da safe, ya kuma kai yarsa Jami'ar Tarayya da ke Jos.

"Yana hanayarsa daga Jos zuwa Keffi a Jihar Nasarawa da yamma ne suka afka wa yan bindiga. Direban ya yi kokarin tserewa amma yan bindigan suka bi su da harbi.

KU KARANTA: Bidiyo da Hotuna: Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto

"Amma akwai wasu masu garkuwar a gabansu kuma suka yi nasarar tsayar da motar suka yi wa direban duka. Farfesan ya roki su tausaya masa saboda sun fusata. Daga nan suka yi awon gaba da shi."

Wani jami'in makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya nemi a taya su da addu'a.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel