Hotuna: Matar Fitaccen Mawakin Kannywood, Ado Gwanja Ta Haifo Santalelen Yaro
- Matar fitaccen mawaki Ado Gwanja, Maryam Zubair Pakii, ta haifi santalelen d'a namiji, wanda suka sanya wa suna Nawab
- Maryam ta yi godiya ga Allah SWT da samun wannan karuwar tare da wallafa hotunan jaririn da kuma ‘yarta ta fari da ta kira Nur
- Masoya da abokan arziki sun taya mawaki Ado Gwanja da matarsa murna, tare da yin addu’ar Allah ya raya yaran cikin Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Ya zuwa yanzu murna ta cika zuciyar fitaccen mawakin Kannywood, Ado Isa Gwanja yayin da matarsa Maryam Zubair Pakii ta haihu.
Wannan ita ce haihuwa ta biyu da matar Ado Gwanja watau Maryam ta yi, kuma a wannan karon, Allah ya albarkace su da d'a namiji.
Matar mawaki Ado Gwanja ta haihu
A wani sako da Maryam Zubair Pakii ta aika a shafinta na Instagram tare da hotunan jaririn, ta yi wa Allah godiya da samun wannan karuwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin hotunan, an ga Maryam tare da jaririn da ta haifa, wanda ta kira shi da 'Nawab' da kuma 'yarta ta fari, wadda ta kira ta da 'Nur'.
"AhmadulilLah" shi ne abin da matar mawakin ta rubuta domin kara nuna godiyarta ga Allah da ya sauke ta lafiya da kuma samun wannan santalelen yaron.
Mutane sun taya Maryam da Gwanja murna
Mutane da dama, musamman ma'abota shafukan sada zumunta sun taya mawi Ado Gwanja da matarsa Murnar samun karuwar d'a namiji.
meerat_sn:
"Muna taya ki muarna. Allah ya raya ya baki lafiyar shayarwa."
sarahmuhd9:
"Allah ya raya miki yaranki Maryam."
sagir_pakii:
"Me ya fi wannan zama abin sha'awa?"
mummy_sultaan:
"Masha Allah. Allah ya rayasu rayuwan addinin musulunci."
who_s.khalifa_:
"Tabarakallah masha Allah. Babbar zuriya, Allah ya raya."
amal_rimee:
"Mabrook mummy Allah ya raya."
meerat_sn:
"Muna jiran sabuwar wakar Maryam da baby @adogwanja."
fulani_naja:
"Allah ya raya mana Nawab."
ys_walia1:
"Allahumma bharik, Allah ya raya baby bisa sunnah."
Kalli hotunan jaririn a nan kasa:
"Ni mijin ta ce ne" - Ado Gwanja
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen jarumi Ado Gwanja ya bayyana cewa ba zai yiwu ya kara aure a yanzu ba, saboda shi yana yin abin da matarsa ta ce.
Da aka tambayeshi kalar matar da yake so, mawaki ado Gwanja ya ce yana son mace wacce ba doguwa ko gajera ba kuma ba siririya ko mai kiba ba.
Mawaki Gwanja ya ce da a ce bai shiga harkar waka da fina-finan Hausa ba, to da watakila zai kasance yana sana'ar mahaifinsa, watau sayar da shayin da ya gada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng