Dandalin Kannywood: Ni mijin ta ce ne, sai abinda matata ta ce nake yi - Cewar Ado Gwanja

Dandalin Kannywood: Ni mijin ta ce ne, sai abinda matata ta ce nake yi - Cewar Ado Gwanja

- A hirar da aka yi da fitaccen jarumin wasan Hausa kuma mawaki a masana'antar Kannywood Ado Gwanja

- An yi masa tambayoyi muhimmai wadanda suka shafi rayuwar shi, inda ya samu damar amsa da yawa daga cikinsu

- Jarumin ya bayyana cewa mahaifinsa ne mai shayin Sarkin Kano

A wata tattaunawa da yayi da BBC, fitaccen jarumi kuma mawaki a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ado Gwanja yayi bayani dalla-dalla akan abubuwan da suka shafi rayuwarshi.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labaran, Ado Gwanja ya amsa tambayar da aka yi masa akan karin aure, inda ya ce: "Gaskiya zai yi wuya ya sake aure, saboda basu yi haka da matarshi ba, kuma shi sai abinda ta ce yake yi," ma'ana dai shi mijin ta ce ne.

Haka kuma da aka tambayeshi irin kalar matar da yake so sai ya ce: "Wacca na aura, amma kuma ina son mace wacce ba doguwa ba, ba gajeriya ba, sannan kuma ba siririya ba, ba kuma mai kiba ba."

KU KARANTA: Tirkashi: Da ya bankawa mahaifiyarshi ciki shege, a yayin da yake gwajin layar bita zai-zai a kanta

Da aka yi masa tambaya kuma dangane da sana'ar gidansu, jarumin ya bayyana cewa: "Ba dan yanzu na zama mawaki ba da tuni watakila ina can ina sayar da shayi, saboda sana'ar mahaifina sayar da shayi ce, ita na gada."

Haka kuma mawakin ya cigaba da cewa mahaifinsu shine mai shayin Sarkin Kano, ya ce sau tari an sha aikensu su kai shayi gidan Sarki ko kuma a turo wani yazo gidansu ya karbi shayi a kaiwa Sarki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng