Kayatattun hotunan sunan diyar mawaki Ado Gwanja da suka dauki hankali

Kayatattun hotunan sunan diyar mawaki Ado Gwanja da suka dauki hankali

Kamar yadda labari ya iso mana, fitaccen jarumin nan kuma mawaki a masana'antar Kannywood da ma bukukuwa, Adamu Isah wanda aka fi sani da Ado Gwanja ya zama Uba.

Allah dai ya albarkaci Ado Gwanja da samun haihuwar diya mace tare da kyakyawar matarsa mai suna Maimunatu.

Anyi bikin suna na gani na fada, inda jama’a suka cika suka tunbatsa a wajen wannan shagali na suna.

Yarinya dai ta suna Asiya Ado Gwanja. Hotunan sunan jaririyar na ta yawo kafofin sadarwa inda ma’auratan suka dauki hankalin jama’a saboda matukar tsaruwa da suka yi tamkar lokacin ne ake bikin aurensu.

Jarumin ya wallafa a shafinsa na Instaram cewa yana godiya ga Allah akan wannan cikar buri nasa.

Ga hotunan sunan a kasa:

Kayatattun hotunan sunan diyar mawaki Ado Gwanja da suka dauki hankali
Kayatattun hotunan sunan diyar mawaki Ado Gwanja da suka dauki hankali
Asali: Instagram

A wani labarin kuma, mun ji cewa Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, kuma wacce tauraruwarta ke haskawa a wannan lokaci, Hadiza Gabon ta taimakawa tsohon nan da hotunanshi suka karade shafukan sada zumunta.

KU KARANTA KUMA: Fariya: Wani dan Najeriya ya yi wa diyarsa shimfida da bandiran takardun Dalar Amurka (Bidiyo)

Jarumar wacce tayi kaurin suna wajen bayar da taimako ga mabukata da masu karamin karfi a jihohin arewa ta taimakawa tsohon ta hanyar sanyawa a gina masa sabon gida.

Dattijon bawan Allah mai suna Abba Babuga dake karamar hukumar Patiskum a jihar Yobe, ruwan sama yayi awon gaba da gidanshi a wani mamakon ruwa da aka tafka a kwanakin da suka gabata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng