Sheikh Rijiyar Lemu Ya Ja Hankali, Ya Hango Baraka tsakanin Najeriya da Nijar
- Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi gajeren tsokaci a game da alakar Najeriya da Nijar
- A ‘yan kwanakin nan, ana ta jifan juna da kalamai marasa dadi tsakanin makwabtan na yammacin Afrika
- Farfesa Rijiyar Lemu ya ce dole a fahimci akwai bambanci tsakanin manufofin gwamnati da ra’ayin jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya tofa albarkacin bakinsa game da rikicin Najeriya da makwabciyarta Nijar.
Kwanan nan aka ji shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya zargi Najeriya da ba gudumuwa wajen yakar kasarsa.
Rijiyar Lemu bai bambanta Najeriya da Nijar
wani bidiyo da yake shafinsa na Facebook, an ji Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya na yin kira ga duk bangarorin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu wanda ya zama Farfesa a makon nan ya ce turawa ne kurum suka raba Najeriya da Nijar.
Duk da iyakoki sun raba mutanen Najeriya da kasar Nijar, malamin hadisin ya yi maganar kafin alakar musulunci da ke tsakaninsu.
Gwamnati dabam da talakan Najeriya
Farfesa Sani Rijiyar Lemu ya ankarar da Nijar cewa ba dole ba ne ayyukan gwamnatin Najeriya ya zama zabin mutanen Najeriya.
A nan ne ya ce hankalin mutanen Arewa ya tashi lokacin da aka ji ana yunkurin amfani da karfin soji saboda an yi juyin mulki a Nijar.
Kira ga malaman jamhuriyyar Nijar
Dalilin jan-hankalin shi ne ganin yadda wasu har da malaman Nijar suka fusata da sabanin da yake neman shiga tsakanin kasashen biyu.
Muddin aka samu wasu a Nijar suna kalamai masu tunzura jama’a, za a iya samun wasu a Najeriya da za su dauki mugun martani.
Kiran Darfesa Rijiyar Lemu ga malamai shi ne su fito su ja kunnen al’’umma, a daina cakuda lamarin siyasa da zamantakewar jama’a.
Yake cewa al’umma ba su da ikon canza manufofin gwamnati don haka ba da yawunsu ne shugabanni suke daukar matsaya ba.
An ji Rijiyar Lemu ya ba da misali da yadda gwamnatin Bola Tinubu ta ke neman kakaba haraji duk da adawar talakawan kasar nan.
“Ya kamata idan mutum mai hankali ne ya bambance duk wani rikita-rikita na siyasar gwamnati da al’ummar kasa.
- Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu
A karshe ya nanata cewa ba za a taba iya raba mutanen Nijar da kuma na Najeriya ba ko da gwamnati ba za ta so ganin hakan ba.
ECOWAS ta karyata gwamnatin sojin Nijar
A wani jawabi, an ji labari cewa ECOWAS ta nuna takaici a game da zargin da ake yi wa Najeriya cewa ta na cutar makwabciyarta Nijar.
Kasashen yammacin Afrika a karkashin kungiyar ECOWAS sun karyata batun cewa sojojin Najeriya na daurewa ta’addanci gindi a nahiyar.
Asali: Legit.ng