Zargin Karkatar da N111.8bn: Majalisar Wakilai Ta Shirya Bincikar Gwamnatin Tinubu
- Majalisar wakilai ta fara bincike kan rashin kawo kayan aikin noma da aka yi yarjejeniya da kamfanin John Deere Tractors
- Rashin kawo kayan aikin ya sa Najeriya ta rasa damarmakin noma biyu, wanda ya janyo koma-baya a shirin tsaron abinci
- Hon. Saba Ahmed, ya bukaci gano inda aka kai N111.8bn na shirin da kuma batun kafa sabuwar masana’antar hada taraktoci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar wakilai ta tsayar da kuduri na binciken rashin kawo sama da manyan taraktoci 2,000 da injinan noma 100.
An sayi kayan aikin ne karkashin shirin inganta tsaron abinci da shirin sabunta dabarun noma na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Majalisa za ta binciki gwamnatin Tinubu
Kudirin, wanda Saba Ahmed Adam (APC, Kwara) ya gabatar, ya nemi kwamitin aikin gona da ya binciki shirin shigo da kayan aikin noman, a cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Saba Adam ya tuna cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya ayyana dokar ta-baci kan tsaron abinci don magance hauhawar farashi.
Ya ce an cimma wata yarjejeniya tsakanin ma’aikatar aikin gona da kamfanin John Deere Tractors don samar da kayan aikin noma na shekara-shekara.
Darajar taraktoci da injinan aikin gonar
Dan majalisar ya ce yarjejeniyar ta kunshi kawo tarakta 2,000 da injinan noma 100, tare da kafa masana'antar hada taraktoci a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan yarjejeniyar tana da darajar $70,041,733.80 (na taraktoci 2,000) da kuma N2,981,739,134.30 (na injinan noma 100).
Hon. Adam ya nuna damuwa cewa shekara guda bayan cimma yarjejeniyar, ba a kawo kayan ba, duk da kuɗin da aka kashe.
Illar rashin kawo kayan aikin noman
Rashin kawo kayan aikin ya jawo jinkiri wajen aiwata da shirin Tinubu na sabunta dabarun noman kasar da kuma samar da isasshen abinci, inji dan majalisar.
Dan majalisar ya kuma koka kan cewa gaza kawo kayan aikin noman zuwa Najeriya, ya sa an rasa damarmakin noman damina da rani.
Hon. Adam ya bukaci a binciki dalilin rashin kawo kayan da kuma matsayin masana’antar hada tarakta da aka tsara kafawa a cikin yarjejeniyar shekarar 2023.
Najeriya na bukatatr tarakta 100,000
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar TOHFAN tace Najeriya na bukatar tarakta 70,000 zuwa 100,000 domin cimma burinta na samar da isasshen abinci a kasar.
Shugaban kungiyar TOHFAN, Alhaji Garba, yace Najeriya na da kimanin eka miliyan 34 na filayen noma wanda ake amfani da su wajen noman rani da damina.
Asali: Legit.ng