Najeriya na bukatar tarakta 100,000, inji Kungiya

Najeriya na bukatar tarakta 100,000, inji Kungiya

Kungiyar masu tarakta da bada hayar kayan aikinta wato (TOHFAN) tace a ranar Talata, kasar nan na da bukatar tarakta tsakanin dubu saba’in zuwa duba dari domin cin mu burin samar da wadataccen abinci.

Majiyar Legit.ng tace Shugaban kungiyar mai suna Alhaji Garba ya shaidawa wa manema labarai a birnin Abuja cewa kasar Najeriya na da kimanin eka miliyan talatin da hudu na kasa wanda ake noma cikinsa.

Tarakta
Tarakta
Asali: UGC

KU KARANTA:Shugaba Buhari ya yi magana kan kashe-kashen jihar Kaduna

A cewarsa, Najeriya na bukatar tarakta dubu bakwai wadanda ka iya aiki a ko da yaushe don taimakawa manoma a lokacin da bukatarsu ta taso.

Ya kara da cewa kungiyarsu, a shekarar 2018, ta samu abinda bai gazawa dubu ashirin da takwas ba na masu son yin amfani da kayan aikinsu amma hakan bai iya samuwa ba inda dubu bakwai kawai suka iya samun dammar amfani da kayan aikin nasu.

Garba yace tsaikon da aka samu ya kasance saboda karancin tarakta a kasar nan, inda ya kara da cewa “A halin yanzu suna da tarakta dari biyar da hamsin da biyu wanda kuma kungiyarsu na da mazauni a jihohi talatin da daya."

"Manoma na neman damar samun kayan aiki daga wajenmu amma sai dai baza mu iya biya musu bukatunsu ba.

A shekarar 2018, mun samu manoma 28,000 sun nemi damar yin aiki da kayanmu amma sai dai manoma dubu bakwai kadaine suka samu dacen samun wadanan taraktoci namu saboda karancinsu a kasar nan.

Muna da eka miliyan talatin da hudu wanda ake nomawa; idan kuwa Najeriya zata kasance abinci ya wadaceta to akwai bukatar ta mallaki tarakta dubu saba’in zuwa dari.

Duba ga abinda muke dashi a kasa yanzu, baza mu iya kula da dukkanin bukatun da ke zuwa garemu domin akalla tarakta bakwai ake da bukata eka dubu goma."

Shugaban kungiyar ya bayyana aniyar kungiyartasu nada shirin karo tarakta dari biyu zuwa dari hudu don bunkasa kungiyartasu da kuma samar da damar amfani da zamani don bunkasa aikin noma kafin karshen watan Afrilu..

Garba ya sake cewa akwai shiryeyen Hadaka tsakanin kungiyarsu da (NAMEL) na a karo tarakta dari biyu ga kungiyar.

Yace, wannan zai taimaka kwarai ga manoma musamman cikin daminar dake tafe.

A wannan shekara, muna da shiri dada karo tarakta gudu dubu daya”.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng