Ana Zargin Kwamishana Da Sace Tarakta 72, Majalisa Tace Kamashi

Ana Zargin Kwamishana Da Sace Tarakta 72, Majalisa Tace Kamashi

  • Majalisar dokokin jihar Neja ta bukaci a gaggauta damke kwamishanan masarautun gargajiya
  • Ana zargin kwamishanan da bada kwangilan gyara taraktoci amma yanzu an nemesu an rasa
  • Cikin Tarakta kimanin 75 da aka bada kwangilan gyarawa, guda uku kadai aka kammala gyara

Minna - Majalisar dokokin jihar Neja, a ranar Laraba, ta umurci jami'an yan sanda su damke Kabir Abbas, bisa bacewar taraktoci 72 na kananan hukumomi 25 na jihar.

Abbas shine kwamishanan kananan hukumomi da harkokin masarautun gargajiya.

A cewar kamfnain dillancin labarai NAN, yan majalisan sun bada shawaran ne a rahoton Malik Madaki, shugaban kwamiti na musamman ya gabatar a Minna.

An kafa kwamitin ne a watan Yuni bayan da aka fara zargin bacewar taraktoci 72.

Hakazalika sun bada shawaran hukunta kamfanin Dogara-ga-Allah Ventures, da aka baiwa kwangilan sabunta taraktocin a 2018.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnonin APC Biyu Sun Dira Patakwal, Sun Sa Labule da Gwamna Wike

tractor
Ana Zargin Kwamishana Da Sace Tarakta 72, Majalisa Tace Kamashi
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayinda gabatar da rahoton gaban majalisa, Madaki ya tuhumci kwamishanan da rashin bin hanyar da ta dace wajen bada kwangilan.

Ya bada shawara a haramta baiwa kamfanin kwangila na tsawon shekaru 20.

Dan majalisan ya bukaci kwamishanan ya bada bayanai da hujjojin dukkan kudaden da aka baiwa dan kwangilan kuma a mayar da kudaden cikin makonni biyu.

Hakazalika kamfanin ya mayar da kudi N2.7m na kudin jigilar taraktocin.

Bayan haka kuma a mayar da taraktoci 3 da aka gyara karamar hukumar Lapai, Chanchaga da Wushishi.

Sauran mambobin majalisar sun amince da wadannan shawari da kwamitin ya bada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel