Tsohon Gwamna a Adamawa Ya ba da Cin Hanci domin Zarcewa a Karo na 2? Gaskiya Ta Fito
- Tsohon gwamnan Adamawa, Boni Haruna ya musanta labarin ba da cin hanci domin zarcewa a zaben 2003
- Tsohon Ministan ya bukaci al'umma su yi watsi da labarin inda ya ce an yi haka ne domin bata masa suna
- Boni Haruna ya ce abin takaici ne yadda masu yada rahoton suka dogara da labarin karya domin cimma manufarsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Tsohon gwamnan Adamawa, Boni Haruna ya yi martani kan zargin ba alkalai cin hanci domin zarcewa a mulki a 2003.
Boni Haruna ya musanta labarin da ake yaɗawa kan ba da cin hanci bayan kotun kararrakin zabe ta kwace kujerarsa kafin mayar masa a 2024.
TABLE OF CONTENTS
Boni Haruna ya shawarci al'umma
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin 16 ga watan Disambar 2024, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya yi kira ga jama'a da su yi taka-tsantsan da labarin da ke yawo a shafukan sada zumunta.
A cewarsa, wannan labarin wanda masu yada shi suka danganta da rahotannin WikiLeaks, babu gaskiya a cikinsa, cewar Peoples Gazette.
Boni Haruna ya ƙaryata ba da cin hanci
"Na yi matukar bakin ciki da irin wannan kazafi na cewa an yi amfani da cin hanci a wani hukuncin da aka yanke a lokacin da Kotun Daukaka Kara ta bayar da hukunci."
"Wannan hukuncin ya kwantar da hankulan al’ummar Adamawa da suka shiga damuwa bayan sakamakon farko a wancan lokaci."
"Irin wadannan kalamai na zargi, kazafi ne kan mutuncina da halayyata, da kuma kan tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, tare da alkalan Kotun Daukaka Kara."
- Boni Haruna
Haruna ya ce abin takaici ne yadda masu yada wannan labarin na karya a cikin rahoton WikiLeaks suka dogara da rahoton tamkar wani littafi mai tsarki.
Boni Haruna ya magantu kan zaben Adamawa
A baya, kun ji yadda tsohon gwamnan Adamawa, Boni Haruna ya ce PDP ba za ta amince da kaddamar da zaben 2019 a matsayin wanda ba kammalalle ba.
Boni Haruna ya ce hukumar zaben ta yi ganawa da jam’iyyar APC a wancan lokaci wanda ya sabawa tsarin dokokin da aka shimfida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng