PDP: Kabiru Turaki ya zabi Boni Haruna a matsayin shugaban yakin neman zabensa na shugaban kasa
A jiya Laraba ne tsohon ministan Najeriya akan aiyuka na musamman, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, ya fito ya bayyana niyyar shi ta fitowa takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2019, karkashin inuwar jam'iyyar PDP
A jiya Laraba ne tsohon ministan aiyuka na musamman, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, ya fito ya bayyana niyyar shi ta fitowa takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2019, karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Sannan ya sanar da zabar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Boni Haruna, a matsayin shugaban yakin neman zaben shi da tsohon ministan harkokin Niger Delta, Dr Steve Oruh, a matsayin mataimakin shugaban yakin neman zaben shi.
DUBA WANNAN: Salah ya tafi Spain neman magani
Sauran mutanen dake da niyyar fitowa takarar sun hada da: tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsoho gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, gwamna jihar Gombe na yanzu Ibrahim Dankwambo da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi.
A zantawar da yayi da manema labarai a Abuja, Turaki yace dukkaninsu sun cancanta kuma duk wanda yaci zaben fidda gwani zai kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.
"Na zauna da dukkansu. Munyi magana, mun fahimci juna. Muna da babbar matsala a kasar nan da 'yan Najeriya ya kamata su dubi jam'iyyar PDP a matsayin jam'iyyar da zata ceton kasar nan.
Idan kuwa 'yan Najeriya sun amince da cewar PDP ce mai cetonsu daga halin da suke ciki, toh dole ne mu kawo musu ceton da suke nema kuma dole ne mu duba bukatun su.
Duk wanda a cikin mu ya samu damar nan, zamu hada kai don taimaka mishi.
A kwanakin bayana ne dai muka kawo muku rahoton cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zabi tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel a matsayin shugaban yakin neman zaben shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng