Tsohon gwamnan Adamawa ya jinjina wa sojoji kan dakile harin Boko Haram a Michika
Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Boni Haruna ya yaba ma rundunar sojoji Najeriya tare da sauran hukumomin tsaro kan matakin mayar da martani kan lokaci da suka yi a hare-haren Boko Haram a garinsa na Michika.
Yan ta’addan Boko Haram a ranar Litinin, sun kai hari garin Michika, hedkwatar karamar hukumar Michika da ke jihar Adamawa kasa da yan kwanaki kadan kafin zaben da za a sake.
Sai dai rundunar sojin sun mayar da harin cikin gaggawa inda suka kasha yan ta’adda da dama tare da dakile harin.
A sanarwar da ya saki dauke das a hannunsa Haruna yace: “Abun damuwa ne ganin Michika ta sake fuskantar irin wannan harin lokacin da kusan mutane sun zauna don sake gina rayuwarsu bayan mamayar da aka kai a 2014 wanda yankin da kusan arewacin kasar suka shiga halin matsi daga hannun yan ta’addan.
KU KARANTA KUMA: Sarkakken lamari: Yadda dan sanda ya kashe wani jami'in Civil Defence
“Zan yi amfani da wannan damar wajen jajantawa mutane, musamman iyalan wadanda suka rasa masoyansu wanda mafi akasarinsu harbin bindiya ne yayi sanadiyar dauke ransu. Ina yiwa wadanda suk ji rani fatan samun sauki sannan kuma Allah ya mayarwa wadanda suka rasa wani abu nasu.
“A cikin irin wannan hali na kunci da radadi da bakin ciki da ya zo, ina bukatar mtanenmu da su kwantyar da hankalinsu sannan suki tawakkali. Wannan lokaci nab akin ciki zai wuce kamar yadda muke fata anan gaba.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng