Zargin Satar Kudi: Kotu Ta Yi Sabon Hukunci kan Shari'ar Ganduje da Gwamnatin Kano

Zargin Satar Kudi: Kotu Ta Yi Sabon Hukunci kan Shari'ar Ganduje da Gwamnatin Kano

  • Babbar kotun Kano ta dage shari'ar Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutum bakwai kan zargin cin hanci da karkatar da kudade
  • Lauyoyin wadanda ake tuhuma sun bukaci karin lokaci don gyara takardunsu, yayin da kotu ta dage sauraron karar zuwa 2025
  • Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta ce za a saurari dukkanin korafe-korafen da suka shafi wannan shari’a a ranar da aka tsayar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Babbar kotun Kano ta dage sauraron shari'ar cin hanci da karkatar da kudin gwamnati da ake tuhumar shugaban APC, Abdullahi Ganduje, zuwa 13 ga Fabrairu 2025.

Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da karar, tana zargin Abdullahi Ganduje da wasu mutum bakwai da laifuffukan cin hanci, karkatar da kudade da almundahana.

Kotu ta yanke hukunci kan bukatar lauyoyin Ganduje na dage shari'ar cin hanci da rashawa.
Kotu ta dage shari'ar gwamnatin Knao da Ganduje zuwa shekarar 2025. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Lauyoyin Ganduje sun nemi alfarmar kotu

Kara karanta wannan

A karo na 6, kotu ta sake ingiza keyar Mama 'Boko Haram' zuwa kurkuku

Wadanda ake tuhuma sun hada da Ganduje, matarsa Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad da wasu kamfanoni uku, inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zaman kotun na ranar Laraba, lauyoyin wadanda ake tuhuma sun gabatar da bukatu daban-daban, lamarin da ya sa aka dage karar don hada bukatun guri daya.

Lauyan Ganduje da wasu mutum biyu, M.N. Duru (SAN), ya bukaci kotu ta cire wata bukata da aka gabatar a ranar 21 ga Oktoba 2024.

Lauyan gwamnati ya soki bukatar Ganduje

“Mun bukaci kotu ta cire wannan bukata. Yanzu muna so mu gabatar da sabuwar bukata da muka rubuta ranar 18 ga Nuwamba”

- M.N Duru SAN

Barista Duru ya kara bayyana cewa akwai bukatar gyara wasu kwanakin da aka rubuta cikin takardar bukatarsu, don haka suka nemi karin lokaci.

Sai dai lauya Adeola Adedipe (SAN), wanda ya wakilci gwamnatin jihar, ya bukaci kotu ta ki amincewa da bukatar Ganduje, ya ce ba a gabatar da ita ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci: Tsohon gwamnan Kogi zai shafe kwana 46 a gidan yarin Kuje

Kotu ta yanke hukunci kan zaman gaba

“Mun gabatar da takarda mai kalubalantar wannan bukata. Don haka muna rokon kotu ta ki amincewa da cire kwanakin,” a cewar Adedipe.

Lauyoyin wasu kamfanonin da ake tuhuma suma sun nemi karin lokaci don gyara takardunsu da hade su guri daya kafin zaman gaba.

Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta dage zaman kotun zuwa 13 ga Fabrairu 2025, inda za a saurari dukkan korafe-korafe guri daya.

APC: Kotu ta dage shari'ar korar Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya a Abuja ta jingine batun yanke hukunci kan shari'ar korar Abdullahi Ganduje daga shugaban APC na kasa.

Wani Saleh Zazzaga ne ya shigar da karar inda yake kalubalantar zaman Ganduje matsayin shugaban APC na kasa saboda ya fito daga shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.