Dangote, BUA Sun Samu Kishiya, China Za Ta Saye Wani Kamfanin Simintin Najeriya
- Wani babban kamfanin China ya saye gaba daya hannayen jarin Holcim da ke a kamfanin simintin Lafarge Afrika a kan $838.8m
- Lafarge na daya daga cikin manyan kamfanonin siminti da kayan gini a Najeriya, watakila tafiyar Holcim za ta iya canja farashi
- Kamfanin China, Huaxim ya shirya amfani da sababbin fasahohi da dabaru domin bunkasa siminti da farashinsa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Lagos - Kamfanin Huaxin na kasar China, zai sayi kaso 83% na hannun jarin Holcim a Lafarge Africa, bayan kayyade darajar hannun jarin kamfanin zuwa dala biliyan 1.6.
Kamfanin ya sanar da cewa zai kashe dala miliyan 838.8 wajen siyan hannun jarin Holcim a Lafarge, yana kiyasta darajar kamfanin tsakanin dala biliyan 1.06 zuwa 1.59.
Rahoton Business Day ya bayyana cewa Huaxin ya bayyana wannan kididdigar a rahotonsa na kasuwar hannun jari ta Hong Kong.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin China ya shigo harkar simintin Najeriya
Kididdigar ta nuna cewa farashin siminti a Najeriya yana tsakanin dala 100 zuwa 150 a kan kowane tan, inda Lafarge ke fitar da tan miliyan 10.6 a shekara.
Huaxin ya kiyasta darajar kadarorin kamfanin simintin Lafarge tsakanin dala biliyan 1.2 zuwa 1.4, tare da darajar kasuwanci da ya kai dala biliyan 1.057.
A cewar rahoton, sayen hannun jarin zai taimaka wa Huaxin wajen fadada harkokinsa a kasashen waje, tare da amfani da sabbin fasahohinsa wajen habaka ci gaba.
Huaxin: Yadda farashin siminti zai karye
Kamfanin Huaxin zai kawo sababbin fasahohi a Najeriya, wanda ake hasashen cewa za su taimaka wajen rage farashin siminti da samuwarsa a kasuwanni.
Tun lokacin da aka sanar da yarjejeniyar ranar 1 ga Disamba, 2024, farashin hannun jarin Lafarge ya karu da kashi 21%, inda ya kai Naira 70.15 a ranar 3 ga Disamba, 2024.
Rahoton Leadership ya nuna cewa akwai yiwuwar sabon tsarin Huaxin zai iya rage farashin siminti a Najeriya, tare da kuma rage tsadar kayan gini.
A halin yanzu, farashin siminti a Najeriya ya tashi sosai, inda ake siyar da buhu mai nauyin kilo 50 tsakanin N7,500 zuwa 8,000.
Duba rahoton sayen kamfanin Lafarge a nan kasa
Farashin siminti ya sauko a Najeriya
A wani labarin, kwanaki mun ruwaito cewa farashin simintin ya ragu a Abuja, Nasarawa da Neja biyo bayan sa bakin da gwamnatin tarayya kan tsadar simintin.
Bincike ya nuna cewa ana siyar da simintin Dangote kan N8,000 da N9,500, Simintin Lafarge N8,000 da N9,300, sai kuma simintin BUA ya kai N7,500 da N9,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng