Karshen Ƴan Bindiga Ya Zo: Najeriya Ta Sayo Manyan Jiragen Yaƙi 12 daga Faransa
- Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da cewa gwamnati ta sayo jiragen yaki kirar Alpha Jets guda 12 daga kasar Faransa
- Hassan Abubakar ya kuma dace NAF za ta karbi jiragen yaki kirar M-346FA, T-129 da kuma wasu masu saukar angulu
- Rahoto ya nuna cewa jiragen Alpha Jets na da tasiri ga ayyukan sojin saman Najeriya, wajen daukar makamai da kai harin kusa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta sayawa rundunar sojin saman Najeriya jiragen yaki kirar Alpha-Jets guda 12 daga kasar Faransa.
Hafsan sojin sama Hassan Abubakar ya sanar da hakan, inda ya ce an sayo jiragen yakin ne daga rundunar sojan sama ta Faransa ta hannun kamfanin SOFEMA.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Hassan ya sanar da sayo wadannan jiragen ne a taron horo da bita kan tsaro da aka shiryawa sojojin sama a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya ta sayo jiragen yaki daga Faransa
Baya ga jiragen Alpha Jets guda 12, hafsan sojin saman ya ce akwai jirage masu saukar angulu kirar T-129 guda biyu da kuma na yaki kirar KA 360i da za a kawo kafin karshen 2024.
A cewar Hassan:
"A shekara mai zuwa, NAF za ta karbi jirage masu saukar angulu kirar AW-109 guda 10, jiragen yaki kirar M-346FA guda 24 da jiragen yaki kirar CASA-295 guda uku da masu saukar angulu na kai farmaki 12, kirar AH-1Z.
"Ba iya nan abin ya tsaya ba. Mun sayo wasu jiragen yaki kirar Alpha-Jetss guda 12, wadanda an yi amfani da su daga rundunar sojin Faransa ta hannun SOFEMA."
Hadimin Tinubu ya jaddada batun sayo jiragen
Olusegun Dada, mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan shafukan sada zumunta ya wallafa a shafinsa na X cewa an kammala shirin kawo jiragen.
Olusegun Dada ya ce:
"A halin yanzu an kammala shirye shiryen jigilar dukkanin jiragen.
"Ya zuwa shekarar 2023, rundunar sojojin saman Najeriya na da jiragen Alpha Jet guda 11 da ke aiki.
"A farkon shekara mai zuwa ne NAF ke sa ran isowar jirgin sama kirar M-346FA 24 da gwamnatin shugaba Buhari ta bayar da kwangilar sayo su."
Wadanne jiragen yaki ne Alpha Jets?
Rahoton shafin Military Africa ya nuna cewa A-Jets wasu jiragen yaki ne da Faransa da Jamus suke hadawa domin kai harin kusa da kuma ba sojoji horo.
Jiragen yaki na Alpha Jets babbar fasahar kirkira ce ta Turai. Kamfanonin Dassault-Breguet a Faransa da na Dornier da ke Jamus ne ke kera jiragen.
Jiragen A-Jets na da tasiri ga ayyukan rundunar sojin saman Najeriya, suna iya daukar makamai iri-iri da suka hada da bama-bamai, rokoki da makamai masu linzami.
Tinubu zai karbo bashi, ya sayo jiragen yaki
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana shirinta na karbo rancen dala miliyan 600 daga masu ba da lamuni.
Gwamnatin tarayyar ta shaida cewa za ta yi amfani da wadannan kudi ne wajen sayo manyan jiragen yaki kirar M-346 kirar Italiya domin yaki da 'yan ta'adda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng