Jerin jiragen Sojin Najeriya 3 da sukayi hadari cikin watanni 3 da suka gabata
Juma'ar yau bata yiwa yan Najeriya dadi ba yayinda shugaban hafsoshin Sojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, ya mutu tare da wasu manyan hafsoshi a hadarin jirgin saman.
Hukumar Sojin saman Najeriya ta tabbatar da faruwar wannan hadari amma ta ce za tayi karin bayani daga baya.
Karo uku kenan a wannan shekarar da jirgin sojin Najeriya zai samu hadari kuma ayi rashin rayukan hafsoshi.
KU KARANTA: Janar Attahiru ya zama shugaban soji na biyu da ya mutu a hadarin jirgi
Ga jerinsu:
1. Abuja
A ranar Lahadi, 21 ga watan Febrairu, jami'an hukumar mayakan sama bakwai sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin Beechcraft KingAir B350i da ya fado a Abuja.
Jirgin wanda ya nufi Minna, jihar Neja domin binciken daliban makarantar GCE Kagara da yan bindiga suka sace ya yi hadari bayan samun matsalan inji.
2. Borno
A ranar Laraba, 31 ga Maris, 2021, jirgin yakin sojin Najeriya Alpha-Jet wanda ke artabu da yan ta'addan Boko Haram ya samu matsala a sararin samaniya kuma yayi hadari.
Matuka biyu sukayi rashin rayukansu sakamakon hadarin.
Yan ta'addan Boko Haram sun yi ikirarin baro jirgin amma bincike ya nuna cewa karya sukayi.
3. Kaduna
A ranar 21 ga Mayu, 2021, jirgin saman NAF Beachcraft 350 dauke da sabon shugaban Sojin Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, da wasu manyan Sojoji ya samu hadari a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa akwai Sojoji 8 cikin jirgin yayinda yayi hadari a tashar jirgin Kaduna.
Kakakin hukumar mayakan sama, Gabkwet, a jawabin da ya saki ya bayyana cewa har yanzu ba'a sa abinda ya haddasa hadarin ba.
KU KARANTA: Shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya ya mutu bayan watanni 4 a ofis
Janar Attahiru ne mutum na biyu da ya mutu kan wannan kujera sakamakon hadarin jirgi.
Na farko shine Laftanan Kanar Joseph Akahan wanda shine shugaban hafsoshin Soji tsaknain Mayun 1967 da Mayun 1968 lokacin da ya mutu a hadarin jirgi mai saukar angulu lokacin yakin basasa.
Asali: Legit.ng