Gwamnatin tarayya Najeriya ta sayo jiragen yaki 14

Gwamnatin tarayya Najeriya ta sayo jiragen yaki 14

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta sayo wasu jiragen yaki 14 domin taimaka wa dakarun sojin kasar wajen murkushe kungiyar Boko Haram

- Gwamnatin ta kuma ce nan bada jimawa ba zata sayo karin wasu jiragen yakin daga kasar Amurka

- Ministan tsaron Najeriya ya ce nan bada jima wa ba zai ziyarci Amurka don tattauna batun sayen jiragen yakin

Gwamnatin Najeriya ta ce ta sayo jiragen yaki kimanin 14 a kokarinta na karfafa guiwar rundunonin sojin kasar wajen tunkarar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba zata sayo karin wasu jiragen yakin daga Amurka domin taimaka wa dakarun sojin kasar wajen murkushe kungiyar Boko Haram.

A halin yanzu dai an gayyaci ministan tsaron Najeriyar zuwa Amurka domin yi wa 'yan majalisar dokokin Amurka bayani kan batun sayen jiragen yakin da kasar ke nema daga Amurkar bayan da a watan jiya gwamnatin Trump ta amince ta sayar wa Najeriya da jiragen yakin.

Gwamnatin tarayya Najeriya ta sayo jiragen yaki 14
Daya da cikin jiragen yakin Boko Haram

Najeriya dai ta shafe shekaru tana fafutikar sayo jiragen yakin daga Amurkar amma gwamnatin Barack Obama ta ki amince wa da bukatar saboda fargabar da ta nuna ta yiwuwar a yi amfani da su wajen keta hakkin bil'adama.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, ministan tsaron Najeriya Mansur Muhammad Dan-Ali, ya ce nan bada jima wa ba ne zai ziyarci Amurkar don tattauna batun sayen jiragen yakin da zarar ya samu amincewar shugaba Muhammadu Buhari game da ziyarar.

KU KARANTA KUMA: Sojin Najeriya sun sake tsarin yadda suke tafiyar da yaki da ta'addanci

Gwamnatin Najeriya ta sha cewa yakin da take yi da Boko Haram yana fuskantar cikas daga tanade-tanaden dokokin Amurka.

Tun a watan Fabrairu ne Shugaba Trump da takwararsa Muhammadu Buhari suka tattauna batun sayar da makaman a wata tattaunawa ta waya da suka yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali ayyukan sojojin saman Najeriya kan 'yan ta'adda Boko Haram

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng