Yaki da ta'addanci: NAF ta kaddamar tare da yin gwajin sabon jirgin yaki (Hotuna)
A kokarinta na cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci da sauran kalubalen tsaro a fadin kasa, rundunar sojin sama (NAF) ta inganta tare da kaddamar da wani jirgin yaki bayan an sake duba lafiyarsa da kara masa karfi.
An kaddamar da jirgin yakin (Alpha Jet), NAF 455, a ranar Asabar 21 ga watan Maris, a wani sansanin atisaye na NAF (407 ACTG) da ke Kainji, kamar yadda Air Commodore Ibikunle Daramola, darektan hulda da jama'a ya sanar a jawabin da ya fitar ranar Asabar da yamma.
Bayan kaddamar da jirgin da aka inganta sassansa, an yi gwaji na musamman domin tabbatar da aikinsa.
Kazalika, an kaddamar da wata hanya mai nisan kilomita 2.8 da aka gina domin sada filin atisaye da dakin kwararrun jami'ai na musamman a sansanin na Kainji.
A jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaban rundunar NAF, Air Marshal Sadique Abubakar, ya bayyana gamsuwa da jin dadinsa a kan inganta jirgin yakin, tare da bayyana cewa hakan zai taimaka a yakin da rundunar ke yi da 'yan ta'adda da sauran batagari.
Ya kara da cewa inganta aikin jirgin yaki a cikin gida Najeriya ya bawa NAF damar tsimin kudade masu yawa idan aka kwatanta kudin da za a kashe idan a kasar waje za a yi aikin.
Kazalika, ya bayyana cewa yin aikin a cikin gida zai bawa kwararrun injiniyoyin NAF damar samu kara kware wa a aiki da kuma nunawa duniya irin basirar da suke da ita.
DUBA WANNAN: Yadda al'amura ke gudana a gidan tsohon sarki Sanusi II a Legas bayan mako guda
Air Marshal Abubakar ya lashi takobin cigaba da gudanar manyan aiyuka a sansanin na Kainji.
Shugaban rundunar ta NAF ya mika godiyarsa ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan goyon baya da gudunmawar da yake bawa bangaren tsaro.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng