Gwamna Ya Ciri Tuta a Arewa, Ya Fara Biyan Masu Nakasa Alawus din N10000 duk Wata
- Gwamna Ahmad Aliyu ya kaddamar da raba keken guragu 500 don tallafa wa masu nakasa da inganta rayuwarsu a ihar Sakkwato
- An tanadi gyaran makarantar AA Raji a kasafin 2025 don samar da yanayi mai kyau ga dalibai masu bukata ta musamman a jihar
- Haka zalika, Gwamna Ahmad ya ce ya fadada shirin ba da alawus din N10,000 na duk wata ga masu nakasa daga 6,6679 zuwa 10,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya kaddamar da raba keken guragu 500 ga masu nakasa don tunawa da 'Ranar Masu Nakasa ta Duniya'.
Gwamnan ya ce ya kaddamar da shirin ne domin tallafawa masu nakasa da kuma tabbatar da shigar kowa cikin ayyukan gwamnatin jhar Sokoto.
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Gwamna Ahmad ya ce rabon keken guragun na daga cikin jajircewar gwamnatinsa wajen kula da bukatun kowa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Sokoto ya rabawa guragu kekuna 500
Gwamna Ahmad ya ce:
"A jiya ne na kaddamar da rabon kekunan guragu guda 500 ga nakasassu a jiharmu, domin bikin ranar nakasassu ta duniya.
Wannan yunƙuri na nufin ƙarfafa mutane da ke da bukata ta musamman da kuma haɓaka haɗin kai a cikin al'ummominmu."
Gwamnan ya ce ya kuma tanadi gyaran makaranta ta musamman ta AA Raji a kasafin kudin 2025 domin samar da ingantaccen yanayi ga daliba masu bukata ta musamman.
Gwamna Aliyu ya fara biyan nakasassu albashi
A cewar gwamnan, ya shirya fadada shirin tallafin N10,000 daga mutum 6,679 da ke cin gajiyar shirin a yanzu zuwa 10,000 domin kara tallafa wa masu nakasa.
"Mun kuma yi tanadin kara wa masu cin gajiyar alawus din N10,000 na duk wata zuwa mutum 10,000 daga 6,679 da ake da su a yanzu.
"Haka kuma, mun kaddamar da sayo kashin na biyu na kekunan guragu domin kara habaka zirga zirga da dogaro da kai na nakasassu a jihar."
- A cewar gwamnan.
Gwamna ta gode wa tsohon gwamna, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, kan tallafin N10,000 da ya ba masu nakasa 6,679 a bikin wannan ranar.
Sokoto: Gwamna zai sayo hatsin N3.7bn
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu ya ware Naira biliyan 3.7 domin sayo hatsi da sauran kayan abinci da nufin tallafawa al'ummar jihar.
Kwamishinan harkokin addinan jihar, Dakta Jabir Maihula, ne ya bayyana hakan, ya ce Gwamna Ahmad ya amince da sayo kayan abincin domin ragewa jama'a radadi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng