Fada da Cikawa: Gwamna Aliyu Ya Fara Rabawa Nakasassu N6,500 Duk Wata

Fada da Cikawa: Gwamna Aliyu Ya Fara Rabawa Nakasassu N6,500 Duk Wata

  • Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu ya cika alƙawarin da ya ɗauka na dawo wa tallafin da ake baiwa naƙasassu kowane wata
  • Bayanai sun nuna tuni aka fara biyan mutane masu lalurar naƙasa N6,500 a wurare daban-daban da aka tanada
  • Ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin ya ce hakan zai taimaka wajen rage yawan barace-barace a kan tituna

Sokoto state - Waraka da tallafi sun fara shiga aljihunan mutane masu naƙasa (PLWDs) yayin da gwamna Ahmad Aliyu ya fara cika alƙawurran da ya ɗauka lokacin kamfe.

Leadership ta tattaro cewa gwamna Aliyu na jihar Sakkwato ya fara biyan mutane masu lalurar naƙasa N6,500 duk wata kamar yadda ya yi alƙawari a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato.
Fada da Cikawa: Gwamna Aliyu Ya Fara Rabawa Nakasassu N6,500 Duk Wata Hoto: BBC Hausa/Facebook
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, a jawabinsa na ranar ranstuwar kama aiki, sabon gwamnan ya yi alƙawarin dawo da ɗan hasafin da gwamnati ke yi wa naƙasassu duk wata.

Kara karanta wannan

Ana Shagalin Babbar Sallah, Gwamna Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata da Babban Shugaba Nan Take

A sanarwan da sakataren watsa labaran gwamna, Abubakar Bawa, ya raba wa manema labarai, ya ce an raba wa mutanen kuɗin a wurare daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoto ya nuna cewa naƙasassun sun cika manyan cibiyoyin rabon kuɗin a kananan hukumomin Sakkwato ta arewa, Dange Shuni da Gwadabawa.

Bawa ya bayyana cewa mutane masu nakasa sun fito sosai a waɗan nan cibiyoyin kuma sun karɓi ɗan albashin N6,500 kowane mutun ɗaya.

Gwamna ya yi abin yabo Inji wani mai naƙasa

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun yaba wa gwamna Ahmed Aliyu bisa dawo musu da tsarin, wanda su ke samun ɗan albashi a kowane wata.

Ɗaya daga cikin nakasassun da suka amfana mai suna, Abubakar Suleiman, ya shaida wa wakilin jaridar cewa:

"Wannan kuɗin da aka bamu zasu taimaka mana matuƙa wajen inganta yanayin rayuwarmu. Dawo da biyan wannan kuɗin duk wata zai rage yawan bara a kan Tituna."

Kara karanta wannan

Masu Yaɗa Jita-Jitar Gwamnan APC Ya Mutu Sun Shiga Uku, Gaskiya Ta Yi Halinta

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun da farko gwamnan ya kafa kwamitin dawo da biyan albashin nakasassun wanda tuni har an ci gaba da biya.

Gwamna Otti Ya Dakatar da Shugaban Ma'aikata da Manyan Sakatarori a Abiya

A wani rahoton na daban kuma Gwamnan jihar Abiya, Alex Otti, ya dakatar da shugaban ma'aikata da baki ɗaya manyan sakatarori.

A wata sanarwa ranar Alhamis, gwamnan ya ce wannan matakin zai fara aiki ne nan take kana ya naɗa muƙaddashin shugaban ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel