Gwamnan Borno ya sanya ma makafi, kurame da guragu 3,127 albashin dubu Talatin-talatin

Gwamnan Borno ya sanya ma makafi, kurame da guragu 3,127 albashin dubu Talatin-talatin

Gwamnatin jahar Borno a karkashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum ta kirkiro da tsarin tallafa ma mutane masu nakasa dake yawon barace barace a jahar, inda ta sanya musu albashin N30,000 a kowanne wata.

Kwamishinan yaki da talauci na jahar Borno, Nuhu Clark ne ya bayyana haka a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba inda yace a cikin watanni biyu da suka gabata, gwamnatin jahar ta kashe naira miliyan 384 wajen biyan wadannan rukuni na mutane.

KU KARANTA: Garkame iyakokin Najeriya: Majalisa ta umarci Hamid Ali ya gurfana a gabanta

A cewar kwamishinan, wannan sabon tsari ya kunshi mabarata da suka hada da kurame, makafi da kuma guragu da yawansu ya kai 3,127 daga cikin mutane 7,000 a duk fadin jahar dake cikin gajiyar wannan tsari na albashin N30,000.

Daga cikin mabaratan akwai guragu 1,550, kutare 357, da kuma kurame 189 wadanda zuwa yanzu sun fara samun kudadensu na wata wata, yayin da makafi 1,037 ke suka fara samun nasu albashin a ranar Laraba, sai dai gwamnati ta kirkiro wannan tsari ne da nufin shirin kaddamar da dokar haramta barace barace a jahar.

Kwamishinan ya kara da cewa baya ga masu nakasa 3,127 dake cin gajiyar wannan tsari akwai kuma wasu rukunin matasa 2,862 daga yankin Jere da Maiduguri da suke samun N30,000 suma a duk wata, amma fa tsarin na tsawon watanni 6 ne kawai.

Daga karshe kwamishina Nuhu Clark yace akwai masu kananan sana’o’I 1,092 da gwamnatin ta raba ma N30,000 a garib Mairi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni ya bada kyautukan motocin alfarma da guraben aikin Hajji ga mahaddatan da suka yi zarra a gasar haddar Al-Qur’ani na jahar da hukumar ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci ta jahar ta shirya.

Mahaddata daga kananan hukumomin jahar 17 ne suka fafata a gasar, yayin da zakaran gasar zai wakilci jahar a babban gasar haddar Al-Qur’ani ta kasa da kasa da za’a yi a jahar Legas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: