Cikakken Jerin Ranakun Hutu Da Yan Najeriya Za Su Mora A Disamba 2024/Janairu 2025
- 'Yan Najeriya za su iya sa ran samun akalla hutun aiki na ranaku uku a tsakanin watan Disambar 2024 da Janairun 2025
- Ana sa ran gwamnatin tarayya za ta ayyana ranar Laraba, 25 ga Disamba, 2024, a matsayin ranar hutu na Kirsimeti, da dai sauransu
- Ana ware ranakun hutu ne domin ba ma'aikata damar hutawa daga aiki wanda zai basu damar kasancewa da iyali da abokan arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A yayin da shekarar 2024 ke shirin karewa, ‘yan Najeriya na ɗokin zuwan ranakun hutu da za a ayyana a watan Disamba 2024 da Janairun 2025.
Gwamnatin Najeriya ta kan ba da hutu ne yayin tunawa da wasu muhimman ranaku ko bukukuwa, da zai baiwa 'yan kasar damar gudanar da wadannan bukukuwa tare da iyalansu.
Disamba da Janairu ba iya watanni ne da ke alamta karewa da farawar shekara ba; suna zama lokacin bukukuwan da ma'aikata ke yin huta daga aiki kuma su yi nishadi da iyalansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin farin ciki, kungiyoyi, hukumomi, ma'aikatu da sauransu suna da al'adar rufe wuwaren aikinsu a duk lokacin da karshen Disamba ta zo.
Duk da haka, ga waɗanda ba a rufe wuraren aikinsu a Disambar, akwai kuma ranakun hutu domin ba su damar yin bukukuwan karshe da farkon shekara tare da iyalansu.
Disamba 2024/Janairu 2025: Ranakun hutu a Najeriya
Legit.ng ta tattaro jerin ranakun hutun aiki da gwamnatin tarayya za ta ayyana a watan Disamba 2024 da Janairun 2025.
Wannan zai taimaka muku wajen tsara yadda za ku gudanar da bukukuwan hutun yadda ya kamata.
1. Disamba 25: Hutun Kirsimeti
A bisa al’ada, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar harkokin cikin gida za ta ayyana Laraba 25 ga watan Disamba a matsayin ranar hutu.
Kirsimeti bikin kiristoci ne na tunawa da haihuwar Yesu Kiristi.
2. Disamba 26: Ranar Dambe
Ranar dambe ita ce ranar hutu da ake yi washegarin ranar Kirsimeti.
Bikin ranar dambe a al'adance da ake yi a Burtaniya da wasu kasashen Commonwealth, ciki har da Najeriya.
3. Bikin sabuwar shekara
Haka kuma gwamnatin Najeriya za ta ayyana hutun sabuwar shekara a watan Janairun 2025.
Janairu 1, 2025, za ta faɗo ne ranar Laraba. Don haka ana sa ran gwamnati za ta ayyana Laraba a matsayin ranar hutu.
Isese: An ayyana karin hutu a wasu jihohi
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa akalla jihohi hudu a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun ayyana ranar hutu a watan Agusta 2024.
An ce jihohin sun ayyana hutun ne domin bikin ranar Isese, wanda ake gudanar da al'adun gargajiya na Yarabawa na asali da kuma kiyaye al'adun Yarabawan.
Asali: Legit.ng