'Arewa Za Ta Yi Mamaya': Gowon Ya Fadi Dalilin Raba Najeriya zuwa Jihohi 12 a 1967
- Janar Yakubu Gowon ya bayyana cewa kirkiro jihohi 12 ya taimaka wajen rage tashin hankali da kawar da tsoron mamayar Arewa
- Tsohon shugaban kasar ya yi wannan bayanin ne yayin ziyarar kungiyar kungiyar Sanata Ibrahim Shekarau a cibiyarsa da ke Abuja
- Gowon ya yi kira ga shugabannin Arewa da su fifita muradun Najeriya, yana mai cewa hadin kai shi ne tushen dorewar dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya bayyana dalilin da ya sa ya kirkiro jihohi 12 a lokacin mulkinsa na soja.
Ya bayyana hakan ne yayin da kungiyar Sanata Ibrahim Shekarau, 'League of Northern Democrats', ta kai masa ziyara a cibiyar Yakubu Gowon da ke Abuja.
"Dalilin kirkirar jihohi 12" Inji Yakubu Gowon
Yakubu Gowon ya ce manufar kirkirar jihohi 12 ita ce rage tashin hankali da kawar da tsoron mamayar Arewa kan sauran yankunan kasar, a cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban kasar ya ce:
“A wancan lokacin mutane sun yi imanin cewa Arewa na son mamaya ne. Da mun ki daukar mataki, da zuwa yanzu mun balle zuwa kasashen Yarbawa, Igbo, Hausa.
“Mun raba Arewa zuwa jihohi domin a kiyaye hadin kan kasa. Duk abin da za ka yi, to ka sanya kasarka a gaba da ra'ayinka."
Gowon ya yi kira ga shugabannin Arewa
Gowon ya ce kirkiro jihohi 12 ne domin hana wani yanki samun karfin da zai zama barazana ga hadin kan kasar baki daya.
Ya yi kira ga shugabannin Arewa da su hada kai kan al’amuran da za su amfani kasa baki daya, maimakon fifita yankunansu kadai.
Ya jaddada cewa dorewar dimokuradiyyar Najeriya na dogara sosai kan Arewa, yana tunatar da irin jagorancin da Firayim Minista Tafawa Balewa ya yi.
Gowon ya kara da cewa akwai bukatar duk wani matakin da Arewa za ta dauka ya zama mai amfani ga hadin kan Najeriya ba iya yankin kadai ba.
Raba Najeriya zuwa jihohi 12 a 1967
Rahoton WikiPedia ya nuna cewa a ranar 5 ga watan Mayun shekarar 1967, Gowon ya sanar da raba yankunan Najeriya zuwa jihohi 12:
- Jihar Arewa maso Yamma,
- Jihar Arewa maso Gabas,
- Jihar Kano,
- Jihar Arewa ta tsakiya,
- Jihar Benue-Plateau,
- Jihar Kwara,
- Jihar Yamma,
- Jihar Legas,
- Jihar Yamma ta tsakiya,
- Jihar Rivers,
- Jihar Kudu maso Yamma, da
- Jihar Gabas ta tsakiya.
'Ina nan da raina' Yakubu Gowon
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) ya karyata rahoton da ake yadawa cewa ya rasu.
A cikin wani sako da hadiminsa ya fitar, Yakubu Gowon ya ce lafiyarsa kalau kuma yana nan da ransa, ya kara da cewa ba gaggawar mutuwa ya ke ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng