An Sauke Sarkin Kano Sanusi II daga Mukamin Khalifan Tijjaniyya na Najeriya?
- Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano, Hon. Sani Auwal Tijjani ya yi bidiyon raddi ga Ibrahim, dan Shehu Dahiru Bauchi
- A cikin bidiyon, Hon. Sani Tijjani ya zargi Ibrahim Dahiru Bauchi da kirkirar takardar karya ta cewar an sauya Khalifancin Tijjaniya
- Kwamishinan ya jaddada cewa Sheikh Mahi Inyass bai sauke Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga Khalifan Tijjaniya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hon. Sani Auwal Tijjani ya yi magana kan takardar da ke yawo na cewa an sauke Sarki Muhammadu Sanusi II daga mukamin Khalifan Tijjaniyya na Najeriya.
Hon. Sani Auwalu Ahmad Tijjani shi ne kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano kuma mai magana da yawun Sheikh Mahi Ibrahim Inyass.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Hon. Sani ya ce takardar da ake yadawa na tube rawanin Khalifancin Sanusi II ta bogi ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga ina takardar sauke Sanusi II ta fito?
Kwamishinan ya yi ikirarin cewa takardar korar Sanusi II daga mukamin Khalifan Shehu Ibrahim Inyass ta fito ne daga Ibrahim, dan Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
"Abin da nake so Ibrahim ya gane, maganarsa yanzu ba ta da tasiri a wajen al'ummar Shehu Ibrahim Inyass a Najeriya. Ba ma yarda da maganar da ka kawo."
- A cewar Hon. Sani.
Kwamishinan ya ce fitar da takardar cewa an sauke Khalifancin Sanusi II yana nufin cewa Shehu Ibrahim Inyass, Shehu Abdullahi, Shehu Ahmad, Shehu Tijjani da Shehu Mahi duk sun yi kuskure.
Hon. Sani ya kara da cewa:
"Gaskiya Ibrahim ka raina Shehu Ibrahim, ka raina mahaifinka Shehu Dahiru Usman Bauchi. Menene Shehu Dahiru zai yi da wani mukami yanzu?
"Kuma a cikin takardar Khalifancin da Shehu Mahi ya rubuta, sai da aka kaiwa Shehu Dahiru Bauchi da Sheikh Sherif Salis, kuma babu wanda ya yi jayayya da takardar."
Shehu Mahi ya amince da sauke Sanusi?
Kwamishinan harkokin addinai ya ce Sheikh Mahi Ibrahim Inyass ya rubuta takardar karyata Ibrahim Dahiru Bauchi, wanda ya jaddada cewa bai sauke Sanusi II daga Khalifanci ba.
"Ka kawo takardu uku kenan, kuma duka karya ce. Babu wadda ban taka na je Senagal ba, kuma Shehu Mahi ya tabbatar da cewa ba shi ya rubuta ba."
- A cewar Hon. Sani.
Mai magana da yawun Shehu Mahi ya nuna cewa Ibrahim Dahiru Bauchi ne kawai ke tayar da jijiyoyin wuta akan an nada Sarki Sanusi II mukamin Khalifan Tijjaniya.
Kalli bidiyon a kasa:
An nada Sanusi II Khalifan Tijjaniya
Tun da fari, mun ruwaito cewa Sheikh Mahi Ibrahim Inyass, babban Khalifan darikar Tijjaniya, ya nada Muhammadu Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniya a Najeriya.
Bangarori biyu na darikar Tijjaniyar sun amince da nadin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) a matsayin Khalifansu a lokacin bikin Mauludin Inyass na 2021.
Asali: Legit.ng