Shehu Inyass ya bayar da gudunmuwa ta bunkasar addinin Musulunci a duniya - Buhari

Shehu Inyass ya bayar da gudunmuwa ta bunkasar addinin Musulunci a duniya - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa jagoran darikar Tijjaniya na Najeriya, Shehi Dahiru Usman Bauchi a sakamakon gudunmuwar ilimin addinin Islama da kuma addu'o'i na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan yayin bikin maulidi da zikirai na shekara da 'yan darikar suka gudanar a biranen Abuja da Kaduna a ranar Asabar din da ta gabata.

Shehu Inyass ya bayar da gudunmuwa ta ci gaban addinin Musulunci a duniya - Buhari
Shehu Inyass ya bayar da gudunmuwa ta ci gaban addinin Musulunci a duniya - Buhari

Buhari wanda ministan ilimi ya wakilta, Mallam Adamu Adamu ya bayyana cewa, ko shakka ba bu Shehu Inyass ya bayar da gudunmuwa matuka wajen bunkasa da ci gaban addinin Musulunci a nahiyyar Afirka, Asia da kuma nahiyyar Turai a sanadiyar wallafe-wallafe na rubutun sa.

KARANTA KUMA: 2019: Mutane 10 da shugaba Buhari ya dogara da su domin samun tazarce

Shugaban kasar ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da goyon bayan duk wata gudanarwa ta kungiyar Tijjaniya domin dorewar zaman lafiya a kasar nan.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito, Buhari ya kuma nemi jagorori da mabiyan wannan darika akan kara zage damtsen su wajen yiwa kasar nan addu'o'i na samun ci gaba da bunkasar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel