Allah ya yiwa babban Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass rasuwa, Buhari ya aika sakon ta'aziyya
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Sheikh Ahmed Tidiane Inyass, babban Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma jagoran darikar Tijjaniya a Afrika.
Wannan na kunshe ne cikin sakon ta'aziyyar da ya aikewa shugaban kasar Senegal, Macky Sall, al'ummar kasar Senegal, da kuma dinbin mabiyan darikar dake nan Najeriya.
Shugaba Buhari ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu yace: "Lallai wannan labari ne mara dadi GA dukkanmu masoyan Khalifa, Sheikh Ahmad Inyass, da ya rasu a Senegal.'
"Sheikh Ahmad Niass, wanda ya gaji mahaifinsa, Sheikh Ibrahim Inyass Ya rike gidan kuma bai kunyata dinbin mabiyan mahaifinsa ba."
"Za a tunashi a bisa ayyukan sa ya yiwa addinin Musulunci da kuma mabiya darikar, da ke da dinbin mabiya a nan Najeriya."
"A madadina, gwamnati da al'ummar Najeriya, ina addu'an Allah ya jikan mamacin."
Shugaban kasa ya tuna lokacin da , Sheikh Ahmed Niass ya ziyarci fadar shugaban kasa dake Abuja a watan Yunin 2018 tare da wasu manyan yan Najeriya, wanda ya hada da shugaban kamfanin BUA< Alhaji AbdulSamad Isyaka Rabi'u.
KU KARANTA: Mun kashe sama da milyan 500 wajen ciyar da yan makaranta lokacin dokar kulle - Ministar Walwala
Sheikh Tijjani Inyass shi ne na hudu a cikin jerin ‘ya’yan Sheikh Ibrahim Inyass . Shi ne Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass na hudu a cikin jerin khalifofinsa tun bayan rasuwar Shehin a shekarar 1975.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ana sa ran gudanar da sallar jana’izar Khalifan a ranar Laraba, a birnin Madinatu Kaulaha da ke kasar Senegal.
Khalifa Sheikh Tijjani Inyass shi ne ya wakilci Shehu Ibrahim Inyass a bikin samun ‘yancin kan Nijeriya a ranar 1 ga Oktoban shekarar 1960. Haka nan ya rubuta littafin a kan Alakar Shehu Ibrahim Inyass da Nijeriya.
Ya rasu ya bar iyalai da yawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng