An Kama Ɓarawon da Ya Sace Kayan Wuta a Masallacin Juma'a
- Rundunar NSCDC ta kama wani da ake zargi ya shahara da sata a masallacin Juma'a na Dakata a karamar hukumar Nasarawa
- Rahotanni sun nuna cewa ana zargin ɓarawon ne mai suna Murtala Aliyu da sace sola a masallacin Juma'ar
- Bayana haka, Murtala Aliyu ya tabbatar da cewa ya taba sace wasu makudan kudi a masallacin Juma'a a Dakata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Jami'an NSCDC sun cafke wani mutum dan shekaru 35 da ake zargi da sata a masallacin Juma'a.
Ɓarawon da ake zargin ya shiga hannu ne yayin da aka kama shi da kayan da ya sato kuma ya gagara bayyana inda ya samo su.
Jaridar Punch ta wallafa cewa kakakin NSCDC a Kano, Ibrahim Abdullahi ne ya fitar da sanarwa kan cafke ɓarawon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama mai sata a masallacin Juma'a
Rahotanni da suka fito daga jihar Kano na tabbatar da cewa an kama wani da ake zargi ya sace kayan wutar sola na masallacin Juma'a.
NSCDC ta bayyana cewa ɓarawon da ake zargin ya haura masallacin Juma'a na Dakata ne ta taga ya tafka satar.
Ɓarawon da ake zargi mai suna Murtala Aliyu ya kasance dan shekaru 35 kuma yana zaune ne a Dawakin Dakata a Kano.
"Wanda ake zargin ya shiga masallacin Juma'a ya sace baturan sola da ke ba wajen ibadar wuta.
An kama shi ne yayin da ya je sayar da baturan da ya sato kuma ya gaza bayyana inda ya samo su ga jami'an NSCDC da ke masa tambayoyi."
- Ibrahim Abdullahi, Kakakin NSCDC
Ko a kwanakin baya ma an zargi ɓarawon da sace makudan kudi har N300,000 a masallacin kuma ya tabbatar da hakan.
Haka zalika NSCDC ta cafke wani matashi mai suna Musbahu Sani da aka zarga da sace wayoyin wutar lantarki a Damarwa da ke Tarauni.
An kama barawo mai sata a makabarta
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta cafke wani matashi da ake zargi da fasa kabari yana sace karafuna.
Matashin dan shekaru 21 ya ce idan ya sace karafuna bayan ya fasa kabari yana sayar da su ne ga baban bola domin samun kudi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng