Barawo ya sace sadaki N100,000 daga aljihun waliyyin amarya a masallacin Al Noor
- Mutanen da suka yi sallar Juma'ar da ta gabata a masallacin Al Noor da ke Abuja sun sha mamaki
- An kama barawon da ya saka hannu a aljihun waliyyin amarya ya kwashe N100,000 na sadaki bayan daurin aure
- An damke shi inda ya sha mugun duka, aka tube masa kaya sannan 'yan sanda suka buga masa ankwa
Jama'a da suka halarci sallar Juma'a a ranar 29 ga watan Janairun 2021 a masallacin Al Noor da ke Abuja sun sha matukar mamaki.
Lamarin mai cike da ban mamaki ya auku ne bayan da aka daura auren wata amarya kuma aka damka kudin sadakinta N100,000 ga waliyyinta amma suka yi batan dabo.
Tuni kuwa waliyyin amaryar ya bayyana batan kudin, lamarin da yasa aka fara caje wadanda ake zargi kuma aka samu kudin a aljihun daya daga cikinsu.
KU KARANTA: Ganduje ya bukaci a haramta yawon shanu daga arewa zuwa kudancin kasar nan
Ganau ba jiyau ba yadda lamarin ya faru ya tabbatarwa da Premium Times yadda aka sanar da daurin auren bayan sallar Juma'a a masallacin Al Noor, inda Sheikh Pantami ke karatu.
Barawon ya gangara zuwa da'irar da masu bada aure da masu karba suke har aka daura. An damka sadakin a hannun waliyyin amarya amma sai ya zura hannu cikin aljihunsa ya sace kudin.
Bayan samun kudin a jikinsa, an yi masa mugun duka sannan aka tube masa kaya kafin daga bisani 'yan sanda su saka masa ankwa.
KU KARANTA: Gwamnan APC ya amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, rai da rai ga masu fyade
A wani labari na daban, an cigaba saka da warwara bayan mutuwar wata mai aiki 'yar shekara 16 a Kano, inda mutane da dama suka yi ta bayar da bayanai akan mutuwar ta.
Wacce suke aiki tare ta sanar da Daily Trust cewa wacce suke yi wa aiki ce tayi ta dukanta har sai da ta mutu.
'Yan sanda kuma sun sanar da yadda suka samu labarin cewa cizon mage ne yayi sanadiyyar mutuwarta, kamar yadda matar da ake zargi ta sanar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng