Gwamnoni 36 za su Haɗa Karfi domin yin Kaca Kaca da Lakurawa

Gwamnoni 36 za su Haɗa Karfi domin yin Kaca Kaca da Lakurawa

  • Gwamnonin Najeriya 36 sun dauki alkawarin samar da mafita da kawo karshen yan ta'addar Lakurawa da suka ɓulla a Arewa
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnonin sun bayyana haka ne bayan wani taro da suka gudanar a birnin tarayya Abuja
  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana matakan da za su dauka inda ya ce za su yi haɗaka da jami'an tsaron Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kawo karshen yan ta'addan Lakurawa na cikin abubuwan da gwamnonin Najeriya suka tattauna a cikin makon nan.

Kafin zaman kwamitin tattalin arziki na kasa, gwamnonin sun zauna a ranar Laraba domin tattauna matsalolin Najeriya.

Gwamnoni
Gwamnoni za su magance matsalar Lakurawa. Hoto: Abdul No Shaking
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnonin sun ce ba za su bari Lakurawa su yadu a wasu yankuna ko jihohi ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba da umarnin rufe makarantu saboda mutuwar Sanata, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni 36 za su yaki Lakurawa

Gwamnonin Najeriya 36 za su hada karfi wajen yaki da yan ta'addar Lakurawa da suka ɓulla a Sokoto, Kebbi da wasu jihohi.

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce kokarin gwamnonin ba zai tsaya kan Lakurawa kawai ba, za su tunkari dukkan matsalolin tsaro.

Uba Sani ya fadi haka ne yayin da yake ganawa da yan jarida bayan kammala taron gwamnonin a Abuja.

"Lallai muna fama da matsalolin tsaro da dama, amma muna magana da jami'an tsaro domin kawo karshensu.
Muna da tabbacin cewa nan gaba kadan za a shawo kan matsalolin. Komai zai zo ƙarshe a nan kusa."

- Gwamna Uba Sani

Bayan matsalar tsaro, gwamnonin sun tattauna yadda jihohi za su yi haɗaka da gwamnatin tarayya wajen inganta ilimin mata.

Tribune ta wallafa cewa Gwamnan ya ce akwai shirin kawo koyon sana'o'i a makarantun Najeriya cikin canjin da ake son kawowa.

Kara karanta wannan

Kwana 1 da sakon Tinubu, Gwamnoni sun shiga ganawar gaggawa, an samu bayanai

Gwamnoni sun gana da Ribadu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jihohin Zamfara da Katsina sun gana da ministan tsaro da mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, ya ce taron ya tattauna yadda za a haɗa karfi wajen dawo da zaman lafiya a Arewa ta Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng