'Yana Kokarin Yin Lalata da Matata,' Magidanci Ya Yi Karar Malamin Jami'ar Bauchi

'Yana Kokarin Yin Lalata da Matata,' Magidanci Ya Yi Karar Malamin Jami'ar Bauchi

  • Wani magidanci mai suna Alhaji Ja'afaru Buba ya shigar da karar wani malamin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi
  • Alhaji Ja'afaru ya zargi malamin da cin zarafin matarsa tare da yin barazanar ba ta matsala a darusansa idan ba ta ba shi hadin kai ba
  • A yayin da malamin da ake zargin ya dauki matakin shari'a, jami'ar ATBU ta yi alkawarin gudanar da bincike don gano gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - An maka wani malamin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi a gaban kotu kan zargin yana cin zarafin wata dalibarsa.

An ce malamin yana koyarwa ne a sashen injiniyancin sinadarai a jami'ar, kuma wadda ake zargin ya ci zarafinta matar aure ce.

An yi karar malamin jami'ar ATBU Bauchi kan zargin cin zarafin daliba, matar aure
Magidanci ya yi karar malamin jami'ar Bauchi kan zargin yana yunkurin yin lalata da matarsa. Hoto: @ATBU_Connect
Asali: Twitter

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa dalibar, ta zargi malamin da aika mata sakonnin batsa, tare da yi mata kalaman batsa hadi da barazana kan karatunta.

Kara karanta wannan

'Kisan mutane 17': Gwamna a Arewa ya hana Fulani daukar fansa bayan harin Lakurawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin malami da cin zarafin matar aure

Mijin matar mai suna Alhaji Ja'afaru Buba ya shigar da karar malamin tare da mika koke ga hukumar ATBU da hukumar rashawa da sauran laifuffuka ta ICPC.

Sakonnin WhatsApp da jaridar ta samu ya nuna yadda malamin ya rika gayyatar dalibar zuwa ofishinsa yana neman ta rungumesa da sauran abubuwan batsa.

A cikin daya daga sakonnin, malamin ya nemi matar auren da ta same shi a wani kebantaccen wuri bayan an tashi makaranta.

An ce tun a farkon shekarar nan abin ya fara, sai yanzu ne dai bayanai suke fitowa.

A cewar mijin matar, jami'ar ta yi alkawarin gudanar da bincike yayin da kuma shi malamin ya dauki matakin shari'a kan zargin cewa ana kokarin bata masa suna, inji rahoton Punch.

An yi karar malami kan zargin lalata

A cikin karar da lauyoyin dalibar suka shigar, an zargi malamin da yin amfani da damarsa ta malami wajen neman yin lalata da dalibar duk da ya san cewa matar aure ce.

Kara karanta wannan

Lalacewar wuta, tsadar fetur da matsalolin da suka jefa talaka a mawuyacin hali

Takardar karar ta ce:

"Malamin da ke koyar da darashin CHE 635 da CHE 656 ya ci zarafin wadda muke karewa duk da ya san matar aure ce, ya sha cewa ta samesa ofis tare da aika mata sakkonnin batsa."

Takardar karar ta yi ikirarin cewa malamin jami'ar ya yi barazanar kayar da dalibar a darasudan da yake koyarwa idan ba ta bashin hadin kai ba.

Da aka tuntubi wanda ake karar, ya ce ba zai iya cewa komai ba tun da maganar na gaban kotu yayin da jami'ar ta yi alkawarin gudanar da sahihin bincike.

An cafke dalibin ATBU da bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan sandan Bauchi sun kama wani dalibin aji uku a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) bisa zargin ya mallaki bindiga da harsashi.

Rundunar 'yan sandan ta ce dalibin, Atim Emmanuel ya dauko bindigar kirar 'pistol revolver' tare da fitowa daga makarantar don fita aikata laifi a cikin gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.