An sallami Farfesa da wani malami daga Jami'ar ATBU ta Bauchi

An sallami Farfesa da wani malami daga Jami'ar ATBU ta Bauchi

- An sallame wasu malamai guda biyu daga jami'ar ATBU da ke garin Bauchi

- Sanarwan korarsu ta fito ne daga bakinm direktan hulda da jama'a na jami'ar, Andee Iheme

- An sallame su ne bayan kwamitin bincike na jami'ar ta tabbatar da sun aikata laifukan da suka sabawa dokar aiki

Mahukuntan Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi sun bayar da sanarwan sallamar wani Farfesa da kuma malamin makarantar guda daya saboda saba wasu dokokin ayyuka.

Mahukuntan jami'ar sun amince da sallamar Farfesa Aminu Ahmed Rufa'i da ke koyarwa a sashin nazarin jikin dan adam 'Humana Anatomy' da kuma Dr. idris Isiyaku Abdullahi da ke koyarwa a sashin koyar da aikin Akanta.

An sallami Farfesa da wani malami daga Jami'ar ATBU Bauchi
An sallami Farfesa da wani malami daga Jami'ar ATBU Bauchi

KU KARANTA: Ana zargin wani dan shekaru 55 da laifin yi wa yaro dan shekaru 8 fyade a Kano

Sanarwan sallamarsu yana dauke ne a wata wasika wanda ke dauke da sannun mataimakin Ragistrar, Aminu Yakubu Gambo.

Wata sanarwa da ta fito ne daga Direktan hulda da mutane na jami'ar, Dr. Andee Iheme yace an kafa kwamitin bincike da ta tabbatar da cewa Farfesa Aminu Ahmed Rufa'i na aiki da aikin dindindin a wani wajen amma kuma ya sake karbar wata aiki na wucin gadi bayan ya wuce shekaru 50.

A kuma taro karo na 86 na jami'ar da akayi a ranar Laraba 25 ga watan Afrilu, Jam'ar ta tabbatar da korar Dr. Idris Isiyaku Abdullahi bayan an same shi da laifin cin mutuncin, karya da bata sunanan jami'ar.

Bayan dakatar da su a nan take, an bukaci malaman biyu su mika dukkan wasu mallakin jami'ar da ke hannunsu tare da katin shaidar aikinsu kafin barin jami'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164