Majalisar Dattawa Ta Tsige Shugaban Kotun da'ar Ma'aikata, Ta Aika Sako Ga Tinubu
- Majalisar dattawa ta yi amfani da wani sashe na kundin tsarin mulkin Najeriya domin korar shugaban kotun da'ar ma'aikata
- A ranar Laraba, 20 ga Nuwamba ne majalisar ta kada kuri'ar tsige Yakubu Danladi Umar daga mukamin shugaban kotun CCT
- An ce majalisar ta tsige Yakubu Umar ne saboda zarge zargen rashawa da kuma rashin da'ar da yake nunawa a aikin ofishinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Laraba, 20 ga Nuwambar 2024 majalisar dattawa ta kori Yakubu Danladi Umar a matsayin shugaban kotun da’ar ma’aikata ta CCT.
Domin tsige Yakubu Umar daga wannan mukami, majalisar ta yi amfani da sashe na 157 (1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa majalisar dattawa ta kada kuri'ar tsige shugaban kotun CCT din saboda abin da ta kira 'rashin da'ar da ba za a iya yafewa ba.'
Majalisar dattawa ta tsige shugaban CCT
A cewar majalisar dattawan, ya zama wajibi a cire Yakubu daga wannan matsayi saboda dabi'unsa ba su dace da mai rike da irin wannan babban mukami ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Korar Yakubu Umar a matsayin shugaban kotun CCT ya biyo bayan samun kashi biyu bisa uku na kuri'un da aka kada a majalisar dattawan.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, (APC, Ekiti ta tsakiya) ne ya gabatar da kudirin korar Umar a matsayin shugaban CCT.
Sanatoci 84 ne suka goyig bayan tsige Umar, kamar yadda Sanata Tahir Monguno, bulaliyar majalsiar ya sanar bayan wani zaman sirri da ya dauki sama da awanni.
Wasu dalilai na tsige shugaban kotun CCT
The Cable ta rahoto cewa Yakubu Umar dai ya fuskanci zarge-zargen cin hanci da rashawa har ma ya ci zarafin wani mai gadi a Abuja a shekarar 2021.
Har ila yau, an zargi shugaban na CCT da rashin zuwa ofis na fiye da wata guda, ba tare da izini ba, kuma ba tare da ya mika ragamar shugabancin ga wani ba.
Sashe na 22 na dokar CCT ya ce shugaban kasa zai iya tsige shugaban kotun ko mambanta ne kawai idan da rubutaccen jawabi daga majalisar wakilai da ta dattawa.
Da wannan matakin na majalisar dattawa na yau, Shugaban kasar zai iya amincewa da dakatarwar da aka yiwa shugaban CCT, Yakubu Umar.
Asali: Legit.ng