Ban yi wa Shugaban CCT komai ba, ya yi mani mugun duka, ya fasa mani baki inji Maigadi

Ban yi wa Shugaban CCT komai ba, ya yi mani mugun duka, ya fasa mani baki inji Maigadi

Mai gadin da shugaban kotun CCT, Danladi Umar, ya ci wa zarafi a ranar Litinin, ya ba jaridar Premium Times labarin abin da ya faru tsakaninsu.

Clement Sargwak mai shekara 22, ma’aikaci ne a kamfanin gadi na Jul Reliable Guards Services Limited, ya na tsaron shagon Banex Plaza a Abuja.

Bayan Danladi Umar ya fitar da jawabi ya na kokarin kare kansa, Clement Sargwak ya shaida wa ‘yan jarida na sa bangaren labarin abin da ya auku.

Mista Clement Sargwak yake cewa:

“Ina aiki ne a matsayin maigadi a wurin ajiye motoci a tsohon sashen shagon Banex Plaza. Ina nan sai wani mutum (Mista Umar) ya zo, na fahimci ya ajiye motarsa a inda bai kamata ba.”

KU KARANTA: Buhari ya bukaci a tabbatar da Salisu Garba a matsayin Alkalin Abuja

“Sai na je wurinsa na fada masa cewa bai ajiye mota inda ya dace ba, saboda ya bar motar a kusa da titi, ta yadda ya hana mutane shigo wa shagon.”

“Bayan na yi masa bayanin abin da yayi, sai ya fito ya mare ni, bayan ya mare ni, sai direbansa shi ma ya fito, ya sharar mani mari, ya keta mani riga, su ka yi ta duka na.”

Sargwak ya ce bai yi wa Umar barazana ba; “Shi ‘Ogan’ ne da kansa (Umar) ya je motarsa, ya dauko wani karfe, ya ce zai rankwala mani a kai.”

Matashin ya ce wani mai shago ne ya rika rokon shugaban na CCT ka da ya buga masa karfen.

KU KARANTA: ‘Yan fashi sun sace kudi da motoci a bankuna a Delta

Ban yi wa Shugaban CCT komai ba, ya yi mani mugun duka, ya fasa mani baki inji Maigadi
Clement Sargwak da Danladi Umar Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Sargwak ya ruga ya je neman mai gidansa amma bai hadu da shi ba. Bayan nan Umar da wani ‘dan sanda su ka saki marinas, su ka yi masa duka.

Da jami’an tsaro su ka karaso, Alkalin ya sake marin Sargwak a gabansu. “Su ka bani umarni in tsuguna, in bada hakuri, na kuma yi hakan.” Inji maigadin.

'Oga' ya doke ni a fuska, ya buge mani baki, sai na fadi. Ana haka ne aka kai mai gadin ofis, karshe ya kare a ofishin ‘yan sanda da ke Maitama, kafin a fito da shi.

Kafin yanzu kun ji cewa shugaban CCT, Danladi Umar da ya doke maigadi a Abuja kwanaki, ya ce yayi masa tsageranci ne, hakan ya sa ya tashi ya kare kansa.

Mai magana a madadin CCT, Ibrahim Alhassan yace maigadin ya gaza bada dalilin da za a hana Umar ajiye motarsa duk da babu wata mota da ta ke wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel