Shugaban CCT ya suburbudi maigadi a Abuja, ya ce yayi masa 'tsageranci'

Shugaban CCT ya suburbudi maigadi a Abuja, ya ce yayi masa 'tsageranci'

- Wani bidiyo da aka ga Danladi Umar, shugaban CCT yana dukan maigadi a Abuja ya janyo maganganu

- Amma kuma kakakin CCT yace matashin maigadin yayi wa Umar tsageranci ne tare da yi masa barazana

- An gano cewa Umar yayi yunkurin adana motarsa a wani wuri amma sai maigadin ya hana shi ba tare da bada dalili ba

Danladi Umar, shugaban kotun sauraron kararraki na musamman (CCT), an ga bidiyonsa yana dukan wani maigadi a Banex Plaza, Wuse 2 dake Abuja.

A wani bidiyo da ya watsu, an ga Umar a fusace inda yake tuhumar wani maigadi. A fusace shugaban CCT din ya dinga haurin maigadin, kafin daga bisani 'yan sanda su hana shi tare da mishi jagora zuwa motarsa.

A yayin martani a kan bidiyon a wata takarda da aka fitar a ranar Talata, Ibraheem Al-Hassan, kakakin CCT, ya ce maigadin tsagera ne kuma yayi barazana ga Umar, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Kudaden fansa ake amfani dasu wurin cigaban Boko Haram, Gwamnoni

Shugaban CCT ya suburbudi mai gadi a Abuja, ya ce yayi masa 'tsageranci'
Shugaban CCT ya suburbudi mai gadi a Abuja, ya ce yayi masa 'tsageranci'. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai farmaki sansanin soji, mutum 9 sun sheka lahira a Dabanga

A yayin bada labarin abinda ya faru, Al-Hassan ya ce "rikcin ya fara ne a kan wurin ajiye motoci wanda shugaban CCT ya tarar babu mota kuma yana kallon wani shago ne da yazo siyayya tare da gyaran waya.

"Bayan da matashin maigadin ya hango shi, ya hana shi saka motarsa a wurin."

Alhassan yace maigadin ya kasa bada dalilin da zai hana Umar saka motarsa duk da kuwa wurin babu komai.

Ya ce alkalin bai nuna ko shi waye ba, "yaron tsagera ne, a yayin da ya tukare shi kuma yayi barazanar cin zarafin shugaban idan bai bar wurin ba."

"Idan da shugaban CCT din ya so tada zaune tsaye ko cin zarafin wani kamar yadda ake yadawa, da ya je wurin da jami'an tsaronsa. Amma sai ya je wurin shi kadai tare da kanin shi," takardar tace.

"Yan sandan da aka gani a bidiyon ba nashi bane. 'Yan sanda ne dake aiki a wurin wadanda suka kai dauki kafin zuwan 'yan sandan Maitama."

A wani labari na daban, zakakuran sojojin sashi na 1 karkashin rundunar Operation Lafiya Dole sun halaka wasu mayakan ta'addanci na Boko Haram a hanyar Njimia dake Alafa, kusa da dajin Sambisa dake jihar Borno.

Kwamandan runduna ta musamman ta 21 dake Bama, Waidi Shayibu, ya jagoranci aikin.

An halaka 'yan ta'addan yayin da suka dasa abubuwa masu fashewa a hanyar da dakarun sojin ke bi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel