Lalacewar Wuta, Tsadar Fetur da Matsalolin da Suka Jefa Talaka a Mawuyacin Hali
Tsadar fetur, kayan abinci da na wutar lantarki, matsalar tsaro da sauransu na ci gaba da zama babbar barazana ga ci gaban Najeriya da 'yan kasarta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Hauhauwar farashin fetur, tsadar sufuri da kuma karancin wutar lantarki sun jawo tattalin arzikin kasar ya durkushe, wanda ya tilastawa 'yan kasa neman mafita.
Talakan Najeriya yana cikin wahala
Najeriya dai na ci gaba da fuskantar tsadar wuta da man fetur, musamman saboda karancin wadatar kayayyaki, faduwar darajar kudi, da kuma sauyawar farashin mai a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur da na wutar lantarki, wanda ya jawo lamura suka kara dagulewa tare da jawo tsadar rayuwa.
Tsadar abinci, rashin ingantaccen ilimi da rashin ayyukan yi ya kara jefa kasar a cikin wani mawuyacin hali, inda kullum ake fama da rashin tsaro.
Ko da yake, gwamnatin tarayya a kullum tana cewa wahalhalun da ake sha na dan wani lokaci ne, manufofin Tinubu za su haifar da d'a mai ido nan gaba kadan.
Matsalolin da ke addabar Najeriya
1. Tsadar man fetur
A shekarar 2022, kudin da Najeriya ke biya na tallafin fetur ya kai Naira tiriliyan 4, kusan 23% na kasafin kudin shekarar (Naira tiriliyan 17.126), a cewar wani bincike da Kingsley Obiora da Peterson K. Ozili suka yi Research Gate ta wallafa.
Sakamakon hakan ne, shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin fetur a watan Mayun 2023. A cewarsa, kasar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin ba.
Rahoton Punch ya nuna cewa janye tallafin fetur da kuma karyewar darajar Naira sun haifar da hauhawar farashin fetur, kayan abinci, sufuri da sauran bukatun 'yan kasa.
Duk da cewa matatar man Dangote ta fara aiki, amma hakan bai sa fetur din ya yi sauki ba, sai ma kara tsada da ya yi daga N650 zuwa kusan N1,010.
Sakamakon tsadar fetur, kungiyoyin kwadago da na fararen hula, sun yi ta kiraye-kiraye na a dawo da tallafin, ko a rage farashin man, amma dai abin ya ci tura.
2. Matsalar wutar lantarki
Bayan tsadar man fetur, babban abin da ke ci wa 'yan Najeriya tuwo da kwarya ba zai wuce matsalar wutar lantarki ba, wanda ta shafi kamfanoni da kananun 'yan kasuwa.
Durkushewar tashar wutar lantarkin Najeriya akai-akai ya sa 'yan kasuwa na kokawa, saboda tsadar amfani da fetur ko gas, wanda ya jawo hauhawar farashin kayayyaki.
Ba iya 'yan kasar ba, rahoton Daily Trust ya nuna cewa, matsalar wutar lantarki ta jawo masu zuba jari daga kasashen waje karaya da kafa kamfanoni a kasar nan.
Sai dai, a baya bayan nan ne muka ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakai na yiwa tashar wutar lantarkin kasar garambawul domin kawo karshen lalacewarta.
3. Hare-haren 'yan bindiga
Rashin tsaro a Najeriya musamman ma a Arewacin kasar na a sahun gaba a abubuwan da ke ciwa gwamnati da 'yan kasar tuwo a kwarya.
Saboda rashin tsaro, noma ya gagara a mafi yawan garuruwan Arewa, wanda hakan ke zama barazana ga wadatuwar abinci a watanni masu zuwa.
Premium Times na ganin cewa matsalar tsaro a Arewa ta samo asali daga kabilanci, yanayin rayuwar jama'a, rikicin addini da kuma fadan makiyaya da manoma.
A baya bayan nan aka samu bullar wata kungiyar 'yan ta'adda mai suna Lakurawa wadda ke addabar Sokoto da wasu jihohin Arewa maso Yamma.
Duk da matakan da jami'an tsaron Najeriya ke dauka na kakkabe 'yan ta'adda a kasar baki daya, har yanzu al'umma na rayuwa ne cikin fargaba.
4. Matsalolin Ilimi a Najeriya
Rashin ingantaccen ilimi na daga cikin matsalolin da 'yan Najeriya ke fuskanta, wadda wasu ke ganin ta na jawo matsalar tsaro, rashin ayyuka da sauransu.
Rahoton UNICEF ya nuna cewa akalla yara miliyan 10.5 'yan shekara biyar zuwa 15 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya, duk da ana ba da ilimi kyauta ne a hukumance a Najeriya.
Marasa zuwa makaranta sun fi yawa a Arewa saboda matsalolin tattalin arziki, al'adu da kuma yadda wasu ke kallon ilimin bokon, musamman ga 'ya'ya mata.
Mun rahoto cewa shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Yahaya Inuwa ya nuna damuwa kan yadda yawan yara marasa zuwa makaranta ke zama barazana ga duk wani ci gaba a Arewa.
5. Rashin ayyukan yi ga matasa
Rashin aikin yi na kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya da ci gabanta kuma hakan ya shafi kokarinta na cimma manufofinta a cewar rahoton Core.ac.uk.
Akwai dalibai da dama da suka juma da kammala karatun digiri amma suna zaune babu aikin gwamnati ko na kamfani, yayin da suka gaza shiga harkokin sana'a.
Sanusi Ya'u Mani da muka zanta da shi ya ce akwai bukatar matasa su cirewa kansu wannan tunanin na cewa za su samu aikin gwamnati idan sun kammala karatu.
Sanusi Mani, wanda shi ne wakilin daliban Durbin Katsina hakimin Mani ya ce kamata ya yi dalibai su koyi sana'o'in dogaro da kai tun kafin su fita daga makaranta.
Rashin ayyukan yi a tsakanin masu ilimi da marasa ilimi ya kyankyasar da bara-gurbin mutane a cikin al'umma, wanda ya kara zama barazana ga tsaro da zaman lafiya.
6. Tsadar kayan abinci
Hauhawar tsadar kayan abinci na ci gaba da karuwa, inda ya kai kaso 33.88 a watan Oktoba 2024. Kayan abinci da dama sun fara gagarar talakan Najeriya.
Rahoton kungiyar tattalin arzikin Najeriya (NESG) ya nuna cewa karyewar darajar Naira, janyewar wasu tallafofin gwamnati sun jawo tsadar kayayyaki a kasar.
Da mu ka tuntunbi Al'ameen Mohammed, wani mai shagon kayan abinci a kasuwar Bacchi, Kaduna, ya shaida mana cewa buhun shinkafa 'yar gida ya haura N90,000.
Al'ameen ya ce akwai nau'ikan shinkafa a kasuwa, amma wadda ta fi kyau ta fi tsada yayin da buhun sabuwar masara ta haura N60,000.
Kwalin taliya kuwa ya haura N21,000 yayin da lita 4.5 na man gyada ya haura N10,000 sannan sukari ya fara gagarar talaka mai karamin karfi.
'A magance matsalolin Najeriya - Kwankwaso
A wani labarin, mun ruwaito cewa Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci shugabanni su gaggauta magance matsalolin Najeriya.
Kwankwaso ya lissafa rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da kuma ƙarancin ababen more rayuwa, musamman wutar lantarki, a matsayin manyan matsaloli.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng