Ku koyi sana'a babu aikin da gwamnati za ta baku, inji wani sanata ga 'yan NYSC
- Santa ya shawarci mambobin bautar kasa da cewa su koma su koyi sana'a su manta da aikin gwamnati
- Ya kuma bukace su da su koma su koyi dinki, girki da sai sauran sana'o'i na halas a fadin Najeriya
- Ya bayyana cewa, hakan ne zai habaka tattalin arzikin Najeriya sannan matasa su iya dogaro da kansu
Abuja - Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Hulda da Jama'a na Majalisar Dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ya shawarci membobin matasa 'yan bautar kasa da su hakaka kwarewar sana'a a maimakon tsammanin samun aikin gwamnati bayan hidimarsu ta shekara guda.
Basiru ya ba da shawarar ne a cikin wata sanarwa mai taken, "Ba da gudummawa ga tattalin arziki ta hanyar habaka kwarewar sana'a," wanda wakilin jaridar Punch a ranar Alhamis 9 ga watan Satumba ya samu a babban birnin tarayya Abuja.
Basiru, a cewar sanarwar, ya yi magana ne a shirin habaka kwarewa da kasuwancin da aka shirya wa membobin bautan kasa a sansanin Koyar da Masu Yi wa Kasa Hidima a Ede, Jihar Osun, ranar Laraba 8 ga watan Satumba.
Sanatan ya shawarci matasa 'yan Najeriya da su habaka kwarewar kasuwancinsu don dacewa da yanayin tattalin arziki na yanzu.
Ya ce:
“Lokacin jiran dimbim damarmakin aiki daga gwamnati ya wuce, ba zai taimakawa tattalin arziki ba."
“Fiye da kashi 70 na kasafin kudin Gwamnatin Tarayya yana shiga cikin biyan bashi kuma akwai karancin albarkatu don yin manyan ayyukan tattalin arziƙi.
"Duk da haka, yanayin bai yi duhu kamar yadda mutane ke rurutawa ba."
Don haka, ya bukaci membobin NYSC da su ba da gudummawa ga tattalin arzikin tare da kwarewarsu wacce ake da matukar bukata.
Ya kuma shawarce su da su fara koyon sana'o'i irinsu dinki, gyara famfunan ruwa, tsara taro, kayan shafe-shafe da abinci da sauransu.
Gwamnatin Buhari zata samar wa matasa masu digiri 20,000 aikin yi mai tsoka
Ana tsammanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai yi wata sanarwa dangane da wani shiri na musamman na matasa masu digiri ranar Talata.
FG ta kirkiri shirin ne da nufin samarwa matasa yan Najeriya da suka kammala digiri 20,000 aikin yi a wasu ɓangarorin gwamnati da kamfanoni a faɗin kasa.
Rahoto ya nuna cewa aikin matasan (yan kasa da shekara 30) zai kwashe watanni 12, kuma za'a basu cikakken albashin masu digiri.
Gwamnatin tarayya na fatan aikin zai taimaka wajen kimtsa matasan da suka kammala karatu domin gobensu da kuma muhallan aiki da zasu iya tsintar kansu nan gaba.
Mai taimkawa shugaban ƙasa ta ɓangaren labarai, Buhari Sallau, shine ya bayyana shirin gwamnatin a wata sanarwa da ya fitar a kafar sada zumunta Facebook.
Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara
A bangare guda, wani rahoton Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama da Tattalin Arzikin Kasa (SERAP) ya ce ‘yan Najeriya miliyan 27 ne ke samun abin da bai kai Naira 100,000 ba a shekara, inji TheCable.
Kungiyar, a ranar Alhamis 2 ga watan Satumba, ta kaddamar da rahoto mai taken ‘Annobar da aka Manta da Ita: Yadda Cin Hanci da Rashawa a bangaren Lafiya, Ilimi, da Ruwa ke jefa 'yan Najeriya cikin talauci.'
A cewar rahoton, ‘yan Najeriya miliyan 56 na fama da talauci kuma 57.205 daga cikinsu galibinsu na dogaro da kansu ne.
Asali: Legit.ng