Gwamna a Arewa Zai Kashe Naira Miliyan 130 a Daukar Nauyin Gasar Karatun Qur'ani

Gwamna a Arewa Zai Kashe Naira Miliyan 130 a Daukar Nauyin Gasar Karatun Qur'ani

  • Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da Naira miliyan 130 domin daukar nauyin gasar karatun Al-Qur'ani
  • Gwamnan jihar Bala Mohammed ne ya sanar da cewa ya ba da izinin fitar da kudin a taron bude gasar da aka gudanar a Jama'are
  • Gwamnan ya ce gwamnatin Bauchi za ta ci gaba da talallafawa gasar domin yaye mahaddata Al-Qur'ani a jihar da kasa baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya fitar da Naira miliyan 130 wajen daukar nauyin gasar karatun Al-Qur'ani mai girma.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ya ba da umarnin fitar da kudin domin ganin an gudanar da gasar karo na 39 a jihar.

Gwamnatin jihar Bauchi ta yi magana bayan daukar nauyin gasar karatun A-Qur'ani
Gwamnatin Bauchi ta kashe N130m wajen daukar nauyin gasar karatun A-Qur'ani. Hoto: Bauchi State Qur'anic Recitation Competition
Asali: Facebook

Da yake jawabi a taron bude gasar a ranar Asabar a garin Jama'are, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen bunkasa karatun Al-Qur'ani, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Lagbaja: A ƙarshe, an birne gawar marigayi tsohon hafsan sojoji a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Bauchi na tallafawa gasar Al-Qur'ani

Gwamnan ya ce kokarin gwamnatinsa na taffalawa gasar zai tabbatar da cewa matasan jihar sun dage da haddace Al-Qur'ani mai girma.

Da ya samu wakilcin shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Sulaiman, gwamnan ya ce:

"Ba za a manta da jihar Bauchi a tarihin gasar karatun Al-Qur'ani a Najeriya ba. 'Yan asalin jihar sun yi shuhura a fagen haddace Al-Qur'ani mai girma.
"Saboda haka, akwai bukatar gwamnatin jihar ta ci gaba da tallafawa gasar karatun Al-Qur'ani domin karfafawa 'yan yanzu da kuma masu zuwa nan gaba."

Kwamitin gasar ya yabawa gwamna

Bashir Khalid Furyam, wanda ya aikowa Legit Hausa da wani bangare na rahoton ya ce shugaban kwamitin gasar na jiha Hassan Zango ya yabawa Gwamna Bala Mohammed.

Furyam ya ce Hassan Zango ya yiwa gwamnan wannan godiya ne bisa goyon bayan da gasar Al-Qur'anin ke samu daga gare shi tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Aiyedatiwa da wasu jerin ƴan takarar gwamna 3 da za su iya lashe zabe

Hassan Zango ya ce kwamitin na iya bakin kokarinsa na ganin an yi adalci wajen alkalancin gasar domin kyankyashe zakarun mahaddata a Najeriya da duniya baki daya.

Wakilin namu ya ce, mahalarta gasar sun fito ne daga dukkanin kananan hukumomin jihar 20 kuma za su fafata a rukuni shida na gasar kamar yadda aka saba.

Kwara: An samu zakarun karatun Al-Qur'ani

A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu gwarazan da suka yi nasara a zagayen karshe na gasar karatun Al-Qurani da aka gudanar a jihar Kwara.

An gudanar da gasar ne a matakin rukunai na daya zuwa na biyar da suka shafi hizib 60 da tajwidi, tafsiri, kira'a da tangimi, a bangaren maza da mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.